Connect with us

SIYASA

’Yan Siyasa Da Yan Kasuwa Sun Nemi Gwamnati Ta Bayyana Sakamakon Zabe Don A Samu Zama Lafiya

Published

on

’Yan siyasa da yan kasuwa a jihar Bauchi sun fara nuna damuwa game da halin matsi da aka shiga na zanga zangar lumana da matasa ke yi saboda gaza bayyana sakamakon zaben da ya gudana ranar asabar din da ta gabata.
A yayin taron manema labarai da kungiyoyin yan siyasa da yan kasuwa suka kira a cibiyar yan jarida wannan larabar sun bayyana rashin gamsuwa da matakin da hukumar zabe da yan sanda ke dauke na shirin sake zabe a wasu wurare lamarin da samun rashin karbuwa a wajen mutane har ake samun jerin zanga zangar kungiyoyin matasa
Shima dkntakarar gwamna na jamiyyar ACPN Injiniya Abubakar Abbas ya koka game da cin zarafin da jamian tsaro ke yiwa yan siyasa jihar Bauchi. Inda ya ce a matsayin sa na dan takarar gwamna na ACPN an jibge shi saboda son zuciya irin na yan sanda da ke karkashin rundunar tsaron ko ta kwana a karkashin Baba Yola.
Don haka ya bayyana cewa halin da ake ciki a siyasance ya fara muni, don haka ya bayyana cewa yadda zabe ya gudana abin gwamnati ta yaba ne kuma ta bayyana sakamakon da mutane suka zaba don a samu wanzuwar zaman lafiya ba tare da shiga cikin fitina ba.Don haka Abubakar Abbas ya ja hankalin gwamnati da hukumar zabe kan ta saki sakamakon ba tare da an sake kashe kudi a banza ba, saboda ko an sake zaben jamiyyar PDP zata sake cinyewa.
Harisu Yakub maigoro mataimakin shugaban kungiyar yan kasuwa ta jihar Bauchi cikin jawabinsa ya bayyana cewa yan kasuwa sun fara damuwa saboda ganin yadda ake neman harzuka mutane yin abin da bai dace ba. Kuma duk abin da ya faru akwai alamun gwamnati ba za ta iya kare musu dukiya ba saboda yadda ake ganin rike sakamakon zaben yana neman haifar da matsala a tsakanin mutane.
Game da batun cin zarafin da yan sanda ke yi, cikin jawabinsa kwamishinan yan sanda na jihar Bauchi Ali Aji janga ya bayyana cewa yan sanda hakkin su ne su hana tashin hankali don a zauna lafiya. Saboda haka yan sanda aikin su suke yi kuma ba za rike hannu suna kallon matasan suna aikata abin da bai dace ba.




Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!