Connect with us

WASIKU

‘Faduwar Ganduje Faduwar Jam’iyyar APC Ne’

Published

on

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a. Barkan ku da aiki, ina muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addu’a Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya. Mulki yana kubucewa uwar jam’iyyar APC ta kasa a jihar Kano, to da wahala APC ta ci gaba da mulkin Nijeriya bayan Buhari ya kammala a 2023.
Amma idan PDP ta karbi Kano, ina hasashen Madugun Kwankwasiyya zai iya komawa jam’iyyar APC da jama’arsa saboda burinsa na takaran shugaban kasa a 2023, to nan ne za a ce APC ba za ta mutu murus ba, saboda Kano ita ce cibiyar APC, kuma wanda ake yin APC don shi ya kammala wa’adinsa, ku rubuta wannan ku ajiye
Bayan jihar Kano, jam’iyyar APC na fuskantar barazanan rasa wasu jihohin, wannan shi ne fahimtata Ban san ko akwai wanda yake da sabanin fahimtata ba. wanna shi ne irin hasashin da na yi.
Sako daga Muhammad Idris, Abuja.
07065279510

‘A Yi Wa Shugaba Buhari Adalci A Kuma Dena Yada Jita-jita’
Assalamu alaikum Editan jaridan LEADERSHIP A Yau Juma’a, Edita ina so ka bani dama na bayyana ra’ayina a kan jita-jitan da ake yadawa. Batun dage zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi a wasu jihohin shugaba Buhari bai da hannu a ciki, duk wanda ya zarge shi babu shakka ya zalunce shi.
Kuma duk wanda ya san ma’anar kalmar ‘INDEPENDENT’ ba zai zargi shugaba Buhari, domin hukumar zabe ta kasa ‘INDEPENDENT’ ce, ma’ana gashin kanta take ci, ba lallai bane shugaba Buhari ya san abin da suke tsarawa. Misali guda biyu rak, ya ishi mai hankali tunani. Na farko: lokacin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wato zaben da aka yi a 2015, wallahi inda ba don hukumar zabe na kasa gashin kanta take ci ba da Buhari bai ci nasara a kan Jonathan ba.
Misali na biyu: zaben shugaban kasa na wannan shekarar 2019, wanda aka dage ranar zaben aka kara sati daya, shugaba Buhari har sai da ya isa mahaifarsa garin Daura da aka dage zaben ya dawo Abuja, kuma duk wanda ya saurari jawabin da shugaba Buhari ya yi a kan batun daga zaben na shugaban kasa, to za a fahimci hukumar INEC gashin kanta take ci, ba a karkashin ikon shugaban kasa take ba.
Wannan shi ne adalcin da duk wani mai hankali ya kamata ya yi wa shugaba Buhari a kan batun soke sakamakon zaben na wasu jahohi da hukumar INEC ta yi.
Sannan batun kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Muhammad Wakili, mutane suna ta yada jita-jita marar amfani domin su haddasa wata fitinar a tsakanin al’umma. Har yanzu ba a cire kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano ba, kuma ba za a cire shi ba, kakakin ‘yan sanda na jihar Kano ya fito ya karyata masu yada jita-jitar.
Amma babu shakka ina tsammani kwamishinan ‘yan sanda na jigar Kano, CP Wakili ya kusan yin ritaya daga aiki, lallai zai bar Kano da zaran ranar ritayarsa ta yi, a ka’ida ma ya kamata tun saura watanni uku kafin ritaya daga aikin dan sanda, doka ta bawa jami’in da zai yi ritaya ya tafi hutu na tsawon watanni uku, shi ne abin da ake cewa “Leabe and Retirement”. Sai dai mafi yawancin manyan jami’an ‘yan sanda da suka kai babban matsayi irin na CP Wakili ba su cika tafiya ‘Leabe and Retirement’ ba, saboda abin da suke samu yake shigo musu ba za su barshi su tafi hutun watanni uku ba, amma kamar karamin jami’in dan sanda da zai yi ritaya yana shan wahalar aiki yawanci suna tafiya wannan hutu na ‘Leabe and Retirement’.
Don haka karku ga nan da wasu lokaci CP Wakili ya bar Kano a zo ana cewa an cire shi ne, a’a ba haka bane ritaya daga aiki ya yi.
Muna fatan Allah Ya maye gurbinsa da wanda ya fishi gaskiya da rikon amana da kuma tsoron Allah, amin.
Sako daga Datti Assalafiy.
08151693170
‘Shawara Zuwa Ga Shugaban ‘Yan Sandar Nijeriya’
Assalamu alaikum Editan jaridan LEADERSHIP A Yau Juma’a, Edita ina so ka bani in bai wa shugaban ‘yan sandar Nijeriya shawara game da rikicin addini da ya addabi jihar Taraba, ga shawara zuwa ga shugaban ‘yan sandar Nijeriya IGP Muhammad Abubakar Adamu.
Maigirma shugaban ‘yan sanda ya dace ka yi nazari a kan jami’an ‘yan sanda da suke aiki a jihar Taraba. Ana samun fadan addini a jihar, inda ake gone gidaje tare da asarar dukiyoyi, daruruwan rayuka na salwanta ba tare da su jami’an ‘yan sandan sun iya shawo kan lamarin. Wannan ya nuna mana cewa akwai wani al’amari boyayye a cikin rundinar ‘yan sandan Nijeriya da suke aiki a jihar Taraba. Babban misali da abin da ya faru a makwanni biyu da suka gabata a jihar, duk wanda yake birnin Jalingo ya ga yadda mabiya wani addini tare da rakiyar jami’an ‘yan sanda a bayansu suna bi suna cutar da wadanda ba addininsu daya ba.
Sawarar da na ke na bai wa shugaban ‘yan sanda shi ne, ya duba sashin rundinar ‘yan sanda masu kwantar da tarzoma (Police Mobile Force) rundina ta arba’in (Mopol 40 Skuadron) da ke Jalingo jihar Taraba, idan da hali a canza musu gurin aiki gaba dayansu cikin gaggawa. Dalilina na fadin haka shi ne; su wadannan ‘Mopol 40 Skuadron’ da ke Jalingo, kashi 91 cikin 100 na yawansu ‘yan asalin jihar Taraba ne mabiya addini daya, sai ‘yan asalin jihar Pilato da Nasarawa su ne suka taru a wannan rundinar ‘yan sanda masu kwantar da tarzoma na jihar Taraba, tun da jimawa ana zargin suna da hannu wajen tayar da rikici a jihar.
Babu wata jiha a Nijeriya da ake nuna banbancin addini cikin aikin tsaro fiye da jihar Taraba, neman halal ya kaini Taraba, na san sirrin tsaron jihar, ina da ta cewa a kan jihar, na san wani shugaban karamar hukuma a jihar Taraba wanda idan an kai jami’in tsaro wanda ba addinisu daya ba a cikin gidansa, ya kan kin amincewa shi saboda tsananin kiyayya. Kuma yau yana daya daga cikin ‘yan majalisar dokoki na jihar Taraba.

Wannan batu na banbancin addini ya shafi kusan komai a jihar Taraba, amma babban abin tashin hankali shi ne, yadda banbancin addinin ya ratsa ya shiga cikin aikin tsaro a jihar, don haka maigirma shugaban ‘yan sandar Nijeriya ka yi nazari sosai musamman kan abin da ya shafi kowani fannin rundunoni na aikin ‘yan sanda a jihar Taraba tare da yin garambawul mai ma’ana.
Yana fatan shugaban ‘yan sandar Nijeriya zai duba wannan lamari sannan ya dauki matakin da ya dace, domin wannan yana kara zubar da kimai aikin ‘yan sanda. Muna rokon Allah ya kawo dauwamamman zaman lafiya a jihar Taraba, amin.
Sako daga Wani Bawan Allah.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!