Connect with us

WASANNI

Mai Koyarwa Ne Ya Cucemu, Cewar Lewandowski

Published

on

Dan wasan gaba na Kungiyar Kwallon Kafa ta Bayern Munchen, Robert Lewandowski ya bayyana cewa yanayin yadda kociyan Kungiyar, Nico Kobac, ya shirya salon wasansu da Liberpool ne yasa basu samu nasara ba tun farko.
Dan wasan yayi wannan bayani ne a ranar Laraba bayan da Kungiyar Kwallon Kafa ta Liberpool tayi waje dasu a gasar cin kofin zakarun turai har gida inda ta lallasa su daci 3-1 Kwallayen da suka fito ta hannun Sadio Mane da Ban Dijk
A wasan farko da Kungiyoyin biyu suka fafata a filin wasa na Anfield dake Kasar Ingila sun tashi daga wasan 0-0 lamarin da dan wasan ya ce kociyan Kungiyar ne ya hanasu fita su kaiwa Liberpool din hari sosai tun a wasan farko.
“Ya kamata tun wasan da muka buga na farko muyi KoKarin zura Kwallo a raga saboda Kwallo a wasan zakarun turai tanada anfani musamman idan ka samu Kwallo a waje ba a gidanka ba” in ji Lewandowski
Ya ci gaba da cewa “Muna da Karfin da zamu iya doke Kungiyar Liberpool amma mai koyarwa ya hanamu fita mu kai hari kuma ga sakamakon abinda rashin fitar ya haifar mana yanzu sai dai mu jira sai shekara mai zuwa”
Sai dai dan wasan wanda yakoma Bayern Munchen daga Dortmund ya bayyana cewa har yanzu suna da damar lashe kofuna guda biyu da suka hada da gasar Bundes Liga da kuma kofin Kalubale na Kasar da suka fito wasan kusa dana kusa dana Karshe sannan kuma suna mataki na farko a akan teburin gasar Kasar maki daya da wadda take mataki na biyu wato Dortmund.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!