Connect with us

LABARAI

Zaben Gwamna: Gwamnan Bauci Ya Gana Da Shugaban Kasa Buhari 

Published

on

Gwamna Muhammad Abdullahi na jihar Bauci ya ziyarci fadar mulkin Nijeriya ta Aso Rock, gwamnan wanda yake fuskantar barazanar muguwar faduwa a sakamakon zaben da yake hannun hukumar zabe mai zaman kanta, ya yi wannan ziyarar ne yau Litinin, kasa da sa’o’i 24 da shugaban kasan ya nesanta kan shi daga yin katsalandan daga ayyukan hukumar zaben.

A ranar Alhamis din da ta gabata mun labarta muku cewar, gwamnan Baucin ya yi ganawar sirri da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, duk da har ya zuwa yanzu ba a san dalilin ganawar ba, amma a yau gwamnan ya shaidawa manema labarai cewa sun tattauna da shugaban kasan ne kan halin da siyasar jihar ta Bauci take ciki ne.

Gwamnan ya bayyana matakin da hukumar INEC ta dauka na janye matsayarta ta farko, wato cewa yanzu ba za ayi zabe karo na biyu ba, maimakon haka za a ci gaba da tattara wancan sakamakon daga inda aka tsaya tun farko, inda gwamnan ya ce wannan matakin zai iya haifar da tashin-tashina a cikin al’ummar jihar ta Bauci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!