Connect with us

KASUWANCI

Asusun Ajiyar Banki Miliyan 36.8 Aka Shigar Tsarin BVN

Published

on

Kimanin asusun ajiya a bankuna miliyan 36.8 ne aka sanya su a cikin tsarin lambar ajiyar bankuna ta BVN a ranar 17 ga watan Fabrairun wannan shekarar.
Shirin hudda a tsakanin bankuna na SS ya nuna cewar, hakan ya nuna yadda suka kai kashi 51 bisa dari na jimlar asusun ajiyar bankuna da suke yin aiki, inda kuma NIBSS ta bayyana cewar, jimlar asusun ajiyar bankuna da suke yin aiki sun kai 71.79.
Lambar shedar ta BVN anyi ta ce ta musamman ga masu yin mu’alama da bankunan dake kasar nan wadda kuma take kunshe da bayanan masu yin ajiya a bankunan dake kasar nan da suka kunshi shedar can yatsun masu ajiyar a bankunan da kuma hoton su.
Babban Bankin Nijeriya CBN ta hanyar kwamitin na ma’aikatan bankuna tare da hadin gwaiwar daukacin bankunan dake kasar nan suka kaddar da shirin a shekarar 2014.
Har ila yau, an samar da tsarin ne don magance satar kudacem masu yim ajiya a bankunan dake kasar nan, bankado dukkan wata almundana da za’a iya akitawa da kuma kara inganta ayyukan bankuna dake kasar nan da sauran su.
Fashin bakin da akayi akan jimlar yawan asusun ajiyarnna bankunan a karshen watan Janairun shekarar 2019, sun kai miliyan 118.9, inda kuma bayanan suka sanar da cewar, an bude manyan asusun ajiya na bankuna har kimanin miliyan 25.97, inda kuma aka bude kanan asusun ajiya na bankuna miliyan 89.67 a cikin watan Janairun wannan shekarar
Darakatan sashen bayanai na Babban Bankin Nijeriya CBN, Mista Isaac Okoroafor an ruwaito yawan asusun ajiya na bankuna a fannin na bankuna akan dalilai da dama, inda ya ce,wanda akafi sank shine, saboda yadda aikin yake daukar lokaci na rufe asusun ajiya na bankuna domin mutane mutane da dama suke yin gaggawar daukar kudaden su da suka ajiye a bankunan su kuma bar asusun masu na ajiya a bankunan babu ko kobo a ciki.
Ya kara da cewar, akwai kuma karancin ilimi da kuma rashin bayar da bayanan wanda zai gaje su idan aka kwatanta da asusun ajiya na bankunan da suke yin aiki.
Bankunan sun kuma yi na’am da ci gaban kudin basu bukatar a tura masu wata riba.
An kuma rauwaito Babban Bankin Nijeriya CBN yana shirin kirkiro da wani sabon shirin da ake kira a turance, (Global Standing Instruction) wanda zai yi aiki da BVN na masu yin ajiya a asusun bankunan dake kasar nan don bankado masu karbar bashin bankuna sannan su kuma ki mayar da bashin sannan kuma suke shirin kara ciwo wani Sabon bashin daga bankunan.
A bisa bayanan da wakilin mu ya samo sun nuna cewar, masu gudanarwar suna shirin wanzar da shirin a cikin wannan shekarar.
Acewar Babban Bankin Nijeriya CBN, shirin na GSI zai bankado da wadanda suka ci bashin sanna kuma suke yunkurin kara ciwo wani sabon bashin, inda kuma za,’a rabawar da daukacin bankunan dake kasar nan bayanan su.
Dabarar zata kuma taimaka wajen duk wani yunkurin da wadanda suka ciwo bashin suka kuma ki maidawa kara ciwo wani sabon bashin daga gun bankunan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!