Connect with us

WASIKU

‘’Yan’uwa Musulmai Sun Manta Da Ahmad Sulaiman A Hannun Masu Garkuwa’

Published

on

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a. Barkan ku da aiki, ina muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addu’a Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya. Ya kamata musulman Nijeriya su fara tunanin nema wa dan’uwansu malam Ahmad Sulaiman mafita cikin gaggawa, amma abin takaici wadanda muke kyautata musu zaton za su yi abin da ya dace wallahi ba su yi ba, domin ina bibiyar duk abin da yake faruwa, abin da ya tabbata ma hatta a kai ziyara ga iyalan malam Ahmad Sulaiman don a jajanta musu a ba su hakuri an kasa yi. Na yi imani da Allah malam Ahmad Sulaiman ba zai taba zaton cewa za a yi wa iyalanshi haka bayan baya nan.
A halin da ake ciki yanzu shi ne, su masu garkuwan sun sauko daga kan naira miliyon dari uku zuwa naira miliyon talatin kudin fansa, tunda har na kusa da malam kun ji yana kuka yana rokon da a sayar da gidanshi da dukkan abin da ya mallaka a biya mutanen da suke rike da shi don ya kubuta, ai wannan ya isheku ku gane cewa malam yana cikin mawuyacin hali. Ku ji tsoron Allah ya ku mutanen da kuka fi kusa da malam Ahmad, ku yi abin da ya dace a kan lokaci, imba haka ba sauran musulmai za su yi daga karshe ku ji kunya.
Sannan mutanen da suke kiran lambar wayan malam Ahmad Sulaiman Kano, sam bakwa kyautawa, asalima cutar da shi kue yi, domin kuna kara jefa shi cikin bala’i da tashin hankali, kamar yadda na ce muna bibiyan halin da malam yake ciki, tun daga karfe 12:00 na daren Talata zuwa karfe 9:20 na safiyar yau Lalata wallahi mutane dabam-dabam sun kira lambar wayan malam, kiran layuka ya shiga wayarsa har guda 153 a tsakanin wannan lokaci (12:00am-9:20am), wannan kiran fa a yau kadai ne.
Haba jama’a kuna ta kiran lambar wayansa a gaban masu garkuwa, hakan bai dace ba, kuskure ne a daure a daina kiran lambar wayansa don Allah, kiran wayansa da ake yi su masu garkuwan hakan zai kara musu karfin gwiwa su ci gaba da rike malam ne, sannan suki rage kudin da suka gindaya saboda za su ga cewa mutum ne da aka damu da shi. Wannan ya kamata ya zama darasi gare mu gaba daya, domin babu wanda ya san abin da Allah zai jarrabe shi da shi a rayuwasa.
Akwai karin bayani da matakin da yanzu haka ake ta nazarin za a dauka don samar wa malam Ahmad mafita tare da abokan tafiyarsa zuwa gobe in sha Allahu.
Muna rokon Allah ya kubutar da su, amin.
Sako daga Mahmud Sani, KD.
08151693170

‘Malaman Kungiyar Izala Ku Ji Tsoron Allah’
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a. Barkan ku da aiki, ina muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addu’a Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya. Wallahi kuka bari Malam Ahmad Sulaiman Kano ya rasa ransa a hannun wadannan miyagun mutane, to duniya sai ta yi Allah wadai da ku, kuma mutunci da darajarku sai ta zube a idon duniya.
Kun daina amsar kiran waya, wasu ma mun samu tabbacin cewa sun fice daga kasar a dai-dai lokacin da dan’uwanku yake bukatar agajinku.
Idan ba za ku iya yin abin da ya dace a kan lokaci ba, to ku bari musulmin Nijeriya su yi abin da ya dace wajen kubutar da shi, a yi abin da ya dace imba haka ba babu wata kara da zamu yi wa wani a kan halin da malam yake ciki, zamu sanar da duniya cewa an yi watsi da malam Ahmad don a kawo masa agaji.
Ya Allah ka bai wa malam Ahmad Sulaiman Kano mafita na alheri tare da abokan tafiyarsa, amin.
Sako daga Datti Assalafy.

‘Shawara Ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari’
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jinni baki daya.
Don Allah Edita ka bani dama na bai wa shugaban kasa muhammadu Buhari shawara a kan zaben shugabannin majalisa. Ya kamata baba ka saka baki a yi zabe nagartacce shugaba, saboda mu talakawa muna tsoron kar a koma gidan jiya, tabbas saka bakin da za ka yi a zaben zai sa a zabi shugabanni da za su taimake ka wajen sauke nauyin talakawan daka dauka. Allah ya sa shugaba Muhammadu Buhari ya amince da wannan shawara tawa, amin.
Sako daga Shehu Mansur Sule Getso, Jihar Kano.
0703707990

‘Kira Ga Masu Yada Jita-Jita’
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jinni baki daya. Ina kira ga mutane masu yada jita-jita a kafafan yada labarai na zamani da su ji tsoron Allah su daina. Mu tabbatar da sahihancin labara kafin mu yada wa duniya. Mu guji yada karya a tsakanin al’umma, domin ita karya tana haifar da rikici tare da rashin kwanciyar hankali. Kafafan yada labarai na zama an maida su wurin yada jita-jita a cikin wannan zamani da muke ciki. To mu sani cewa duk rikicin da muka haddasa sakamakon yada jita-jita sai Allah ya tambaye mu. Don haka ina kira ga mutane musan irin labarin da zamu dunga yadawa ko kuma su san sahihancin labara kafin mu yada.
Sako daga Saminu Mayentea Batsari.
08036773485
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!