Connect with us

MANYAN LABARAI

Nijeriya Ta Kori ’Yan Kasar Ghana Hudu

Published

on

Jiya juma’a Hukumar kula da shige da fice ta kasa NIS ta bayyana cewar, ta kori ‘yan kasar Ghana su hudu daga cikin kasar nan saboda saba wa dokokin hukumar daban-daban.
Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawun Hukumar Sunday James ya sanya wa hannu ya kuma rabarwa manema labarai.
Ya bayyana cewar, Ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau ya amince da korar ‘yan kasar ta Ghana daga kasar nan.
A cewarsa, an yi korar ce a bisa karfun ikon da sashe na 45 (1) a cikin baka da kuma (2) a cikin baka na Hukumar na shekarar 2015 da ta bai wa ministan ikon yin korar.
Wadanda aka korar sun hada da maza uku da kuma mace daya Florence Donkur, Simon Gyan, Yeboah Collins da kuma Alhaji Isa.
James ya ci gaba da cewa, an mayar da su kasarsu ta Ghana ta hanyar filin jirgi na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke garin Abuja a yau juma’a 22 ga watan Maris na shekarar 2019 da karfe tara na safe.
A cewar kakakin Kwantirola Janar na Hukumar Muhammad Babandede tuni ya tabbatar da korar yan Ghanan daga kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!