Connect with us

KASUWANCI

NNPC Ta Fara Gyaran Matatar Mai Na Fatakwal

Published

on

Kamfanin NNPC ya sanar da cewar, ya fara gayaran matatar ta Fatakawal kashi na farko yadda zasu dinga samar da danyen mai ganununa guda 210,000 a kullum.
Sanarwar wadda aka fitar da ita a ranar Alhamis data gabata ta ce, matatar man ta Fatakwal har ila yau, zata samar da gangunan danyen mai 60,000 a kullum an kuma gina ta ne a shekarar 1965, inda a lokacin take samar da gangunan danyen mai 150,000 an kuma kaddamar da ita ne a shekarar 1989.
Babban Manajin Darakta na rukunonin kamfanin na NNPC Dakta Maikanti Baru ne ya kaddamar da fara aikin a matatar man ta Fatakwal a ranar Alhamis data gabata bayan an shafe shekaru 19 ba sake yi mata wani gyra ba.
Bayanin na Dakta Maikanti Baru wanda Janaral Manaja na sashen hudda da jama’a Ndu Ughamadu ya fitar a garin Abuja ya bayyana cewar, kamfanin Milan-based Maire Tecnimont S.p.A tare da hadin gwaiwar kamafin cikin gida Tecnimont Nigeria aka baiwa kwangilar aikin.
Acewar NNPC, kamfanin Maire Tecnimont S.p.A an sanya sunan sa a jiren kamfanonin a kasuwra musayar kudi ta kasa.
Snarwar ta ci gaba da cewa, kamfanin Tecnimont Group yana gudanar da ayyukan sa a kasashe 40 dake fadin duniya kuma yana da ma’aikanatn da yawan su ya kai kimanin 5,500.
Baru ya sanar da cewar, ana sa rana a zagayen aikin na farko, aikin na sarrafa danyen mai zai kai yawan kashi 60 bisa dari.
NNPC ya kara da cewa, ya janyo kamfanin Eni/NAOC don ya dinga bayar da shawara akan gyran matatar man ta Fatakwal.
Acewar sanarwar, aikin kashi na farko zai shafe watannin shida zai kuma hada da duba kayan aikin kuma a cikin karashen watan Maris na shekarar 2019 za’a fara gudanar da aikin.
Sanarwar ta kara da cewa, aikin kashi na biyu kuma kamafnin Engineering Procurement Construction tare da hadin gwaiwar kamfanin JGC na kasar Japan ne zasu aiwatar dashi.
Da yake yin jawabi a madadain sauran yan kwangilar, wani jami’ai mai suna Antonio Bella dake aiki a kamafnin Eni ya ce, dukkan kamfanonin da zasu gudanar da aikin zasu tura kayan aikin su zuwa matatar don tabbatar da an fara aikin a cikin nasara.
Suma da suke nasu jawabin a madadin kaungiyoyin ma’aiakata shugaban kungiyar PENGSSAN Odor Ayiri, da kuma shugaban kungiyar NUPNNGW Dibiah Joseph sun yi alkawarin baiwa ma’aiktan goyon bayan da ya dace wajen gudanar da aikin.
In ba’a manta ba kamafnin na NNPC tuni ya yi watsi da tsarin zuba kudi da yake yi a baya soboda yawan bukatar da ake gabatar masa ta kusan watanni sha biyu na tattaunawa.
Kamafnin na NNPC ya kasance ya koma yana biyan kudin kai tsaye, ya kuma kasnace ya rarraba aikin zuwa kashi kashi tare da farawa akan matatar mai ta garin Fatakwal sannan kuma a wuce ga matatar mai ta garin Warri data jihar Kaduna ta hnyar yin amfani dabaru iri daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!