Connect with us

MANYAN LABARAI

NUJ Ta Zabi Sababbin Shugabanni A Zamfara

Published

on

Kungiyar ‘Yan jaridu ta kasa (NUJ), reshen Jihar Zamfara, ta zabi sabbin shugabannin da za su jagoranci kungiyar har nan da shekaru uku.
Shugaban kwamitin shirya zaben, Malam Sale Kurya-Madaro, ne ya shelanta sakamakon zaben, inda ya ce, Abdulrazak Bello, na rediyon Pride FM da Bello Buko, na ma’aikatar yada labarai na Jihar ne aka zaba a matsayin shugaba da mataimakin shugaba ba tare da jayayya ba.
Haka nan, Abubakar Ahmed, na kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), an zabe shi a matsayin Sakataren kungiyar a karo na biyu, bayan ya kayar da mai ja da shi da kuri’u 81 inda wancan ya sami 62.
Kurya-madaro, ya kuma shelanta Jamilu Tsafe, na jaridar Legacy, a matsayin wanda ya yi nasara a matsayin ma’ajin kungiyar da kuri’u 58 a kan mai ja da shi da ya sami kuri’u 49 dayan kuma ya sami 37.
Ya kuma bayyana sauran wadanda aka zaban ba tare da jayayya ba, da suka hada da Nasiru Aula Dabbakal, na gidan Rediyon Jihar ta Zamfara, a matsayin mataimakin Sakatare, Abubakar Maiturare, na gidan talabijin NTA, a matsayin Sakataren kudi da Aliyu Sanda, na ma’aikatar yada labarai ta Jihar a matsayin mai binciken kudi.
Daya daga cikin masu neman shugabancin kungiyar, Jamilu Birnin Magaji, wanda ya taba zama Sakataren kungiyar, ya janye ne daga takaran ana gab da fara zaben.
Birnin Magaji, wanda yake da magoya baya masu yawa a lokacin yakin neman zabensa, ya ce an matsa masa ne daga ciki da kuma wajen kungiyar a kan ya janye daga takaran.
An dai gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, dalilin da ya sanya sakamakon zaben ya zama karbabbe ga kowa.
Kwamitin ya gudanar da zaben ne a kan sa idon wakilai daga shalkwatar kungiyar ta kasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!