Connect with us

KASASHEN WAJE

Sabon Harin Isra’ila A Gaza Ya Hallaka Mutum 7

Published

on

Rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila (IDF) ta yi ruwan bama-bamai a zirin Gaza , bayan da wadansu mayaka suka harba wasu rokoki cikin kasar.

Dakaraun haramtacciyar kasar Isra’ila din sun bayyana cewa sun kai hari ne a ofishin shugaban kungiyar Hamas da kuma ofishin binciken sirri na kungiyar.

Hukumar kula da lafiya ta Gaza ta bayyana cewa mutum bakwai sun jikkata sakamakon harin.

Rahotanni sun bayyana cewa; bayan tsagaita wuta na wani lokaci sai mayakan suka sake harba wasu rokoki zuwa cikin haramtacciyar Isra’ila wanda hakan ya jawo martani daga kasar.

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin harba rokokin inda daya rokar ta fada a wani gida a Mishmeret, kudancin Tel Aviv a jiya Litinin.

Sojin haramtacciyar Isra’ila sun zargi Hamas da harba rokokin inda wani babban jami’in Hamas ya musanta zargin. Wannan na zuwa ne bayan da aka kwashe makonni ana takaddama tsakanin sojojin Isra’ila da masu zanga-zanga a iyakar kasashen guda biyu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!