Connect with us

SIYASA

Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Da Aka Shigar Kan Zababben Gwamnan Borno

Published

on

Wata babban kotun tarayya da ke da matsuguni a garin Maiduguri a jiya Talata ne ta yi watsi hadi da korar wani karar da aka shigar a gabanta da ake neman kotun ta soke zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC a jihar Borno.
Kamfanin dallacin labarai ta kasa NAN, ta shaida cewar karar wanda wani kusa a jam’iyyar APC Alhaji Mamman Durkwa ya shigar a gaban kotun a ranar 19 ga watan Disamban 2018 da ke neman a soke zaben fitar da gwani na jam’iyyarsu.
Alhaji Durkwa dai ya kalubanci nasarar da zababben gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum, ya samu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar ta APC a ranar 30 ga watan Satumban 2018.
An shigar da jam’iyyar APC da hukumar zabe mai zaman kanta INEC dai a cikin karar da aka shigar din.
Da yake yanke hukuncinsa kan karar, Justice Jude Dagat, ya ce, kotun ta yi watsi da wannan karar ne a bisa gaza gabatar da karar a cikin kwana 14 da mai shigar da karar ya gaza yi kamar yadda dokar zabe ta adana.
Dagat ya shaida cewar karar da aka shigar gabanin zabe dole ne ya zama na cikin tsarin da doka ta adana.
Ya ce, an gabatar wa kotun karar ne bayan karewar wa’adin da doka ta ware domin shigar da irin wannan karar.
Mai shari’ar ya kori karar ne da kuma bayar da umurnin kwanaki 30 ga dukkanin wanda bai gamsu da hukuncin ba da cewar yana da damar daukaka kara amma a cikin wata guda.
Lauyan kariya Barista Abdulwasiu Alfa, ya nuna farin cikinsu kan wannan hukuncin, inda kuma lauyen mai shigar da kara Usman Abubakar, ya ce za su daukaka kara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!