Connect with us

LABARAI

Hatsarin Mota: Masu Zuwa Shan Maganin Bindiga Zamfara 19 Sun Mutu A Hanya

Published

on

Shan maganin Bindiga da alumar ke tatururuwa zuwa kauran Tsauni da ke gundumar ‘Yan Kuzo a karamar hukumar Tsafe jihar zamfara ya yi sanadiyar mutuwar mutum goma sha tara,talatin da takwas kum sun samu munan raunuka, Mutanen dai sun fito ne daga karamar hukumar Rafi cikin jihar Neja.Wannan hadarin ya auku ne a Daudawa cikin karamar hukumar Faskari jihar Katsina.
Kwamadan Hukuma Kare hadura ta kasa na Shiyar Funtuwa, Joshua Bulus Ako ya tabbar da afkuwar wannan hadari tare da mutuwar mutum goma sha tara, kuma mutum talatin da takwas na kwance a Asibitin karamar hukumar Funtuwa .
Kwamanda Joshua Bulus ya kara da cewa ‘ Hadirin ya faru ne da misalin karfe bakwai na safiyar jiya Juma’a, a Daudawa cikin karamar hukumar Faskari mai nisan kilomita goma sha biyar tsakanin garin da karamar hukumar Funtuwa. Ya ce, sun isa wajen hadarin jim kadan da farwarsa, suka kuma dauko masu raunika zuwa Asibitin Funtuwa.
Kamar Yadda bayani ya nuna Hadarin ya faru ne sakamakon baccin da dareban ke yi tare da gudu babu kaukautawa. Mortar kirar Mitsubishi Kanta mai lamba, DK 654 ZP na dauke da mutum sitin a cikinta yayin da ta yi wannan mummunan hadarin, in ji Joshua.
Haka kuma ya nuna matkar damuwarsa bisa yadda ake cunkusa al’umma cikin mota, wanda ke sanadiyar mutuwar mutane da dama. Saboda haka sai kara kira ga jama’a das u guji yin haka domin tsira da rayuwarsu, sannan kuma ya gargadi direbobi das u ci gaba da tafiya cikin nutsuwa.
Tuni dai Shugaba karamar hukumar Funtuwa, Malam Lawal Sani Funtuwa ya dau nauyin maganin masu raunuka da kuma mai da Gawarwakin garuruwansu.
Xaya daga cikin wadanda wannan hadarin ya rutsa da shi Kuma yanzu haka ya Asibitin Funtuwa kwance, mai suna Buhari Usman Gani, ya bayyana wa wakilinmu cewa ‘ Sun fito ne daga karamar hukumar Rafi cikin jihar Neja kuma dukkansu ‘yan kungiyar sa-kai ne “Mun je Tsafe don shawo magani Bindiga kuma mun Shawo a waje komawarmu gida ne wannan hadari ya auku”.
Yanzu haka dai jama’a ke tatururuwa zuwa wajen amsar maganin Bindigar musamman ‘yan kungiyar sa-kai daga sasan Arewacin kasar nan don kare kai daga harin’yan bindiga da ke cin karensu babu babaka a jahar Zamfara da Katsina da Kaduna da Sakkwato da kuma Neja.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!