Connect with us

KASUWANCI

Tattalin Arzikin Nijeriya: Bankin Bayar Da Lamuni Na Duniya Ya Yi Amai Ya Lashe

Published

on

Bankin bayar da lamuni na duniya , IMF, ya bayyana cewar, tattalin arzikin Nijeriya zai dinga fada-fada da sauri sabanin kirdagon da bankin ya yi a baya na cewar, tattalin arzikin Nijeriya zai ragu.
Bankin a cikin rahoton sa nayim dubi akan tattalin arzikin duniya WEO da ya fitar a ranar Talatar data wuce a taron da ake ci gaba da gudanarwa na Bankin na IMF da kuma rukunonin Bankin Duniya ya ce, tattalin arzikin Nijeriya zai karu zuwa kashi
2.1 bisa dari a shekarar 2019, India hakan ya nuna cewar, an can samu karin kashi 0.1 daga kaahi 2 biya dari da Bankin ya yi kirdado za’a samu a watan Janairu.
A rajoton na WEO da aka fitar a wanatan Janairu Bankin ya rage yawan tattalin arzikin Nijeriya saga kashi 2.3 bisa dari a cikin watan Okutobar shekarar 2018 zuwa kashi 2 bisa dari, Inda ya dora laifin akan samun raguwar farashin mai.
Har Ila yau, Bankin ya yi kirdadon tattalin arzikin nahiyar Afirka zai daga zuwa kashi 3.5 bisa dari a shekarar 2019 zuwa kashi 3.7 nisa dari a shekarar 2020 daga kashi 3 bisa dari a shekarar 2018.
Kirdadon ya kai kashi 0.3 da kashi 0.2 bisa dari kasa da a shekarar 2019 zuwa shekarar 2020 fiye da a cikin watan Okutobar shekarar 2018
A karahe rahoton ya ce, ana sa ran tattalin arzikin Nijeriya dana kasar Angola zasu karu zuwa kimanin kashi 2.6 bisa dari da zuwa kashi 3.9 a gajeren zango.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!