Connect with us

RAHOTANNI

Tarihin Zuwan Turawa Zariya

Published

on

Tun gabannin mamayar turawa ga daular Zazzau, an samu cewa karfin daular ya ragu nesa da yadda ta kasance a baya sabili da wasu dalilai. Da farko dai, akwai rikicin cikin gida da ya mamaye kabilun Fulani da suka jagoranci karbe ikon Zazzau a zamanin Jihadi saboda neman mukami.
An ce tun zamanin Sarki na farko aka soma wannan sabanin tsakanin jagora kuma sarkin Zazzau na farko Mallam Musa da wani Ja’e shugaban kabilar fulani Yesgwamawa, amma sai aka ba shi sarautar Kajuru aka zauna lafiya.
Daga baya sai rikicin ya sake kamari bayan rasuwar sarkin Zazzau Usman Yero, a wajajen shekara ta 1897 kenan.
Hakan ya samu ne ta yadda kabilu hudu na Fulani da aka sani da mulkin Zazzau suka nuna bukatarsu ga mulkin, kabilun su ne Mallawa, Katsinawa da Barnawa.
A cikin masu neman mulkin akwai dan marigayi Sarki Yero mai suna Madaki Kwasau, sai Mallam Lawan dan tsohon Madaki da kuma wani daga cikin ‘ya’yan tsohon sarkin Zazzau Mallam Sambo.
Babban abin da kuma ya samar da sabani a lokacin shi ne, yadda Galadima ya tsaya kai da fata cewar wani kurma kuma Makaho mai suna Mallam Muhammd ya kamata a bai wa sarauta. Mutane sun ce hakan na da nasaba da kokarinsa na dora wanda ba zai iya katabus ba a mulki ta yadda zai rinka juya shi.
Ganin karfin ikonsa ya sa wadancan kabilu na Fulani suka dunkule tare da goya wa Madaki kwasau baya domin ya zama sarki. A kan haka suka nemi gudunmuwar sarkin Kano Aliyu Babba, da kuma rundunar ‘yan bindiga da mahaifin Madaki Kwasau ya kafa a zamanin rayuwarsa, shi kuwa Galadima sai ya nemi goyon baya daga Sakkwato.
Ana cikin wannan kiki-kaka, sai wazirin Sakkwato Buhari ya zo Zazzau da niyyar masalaha. Ya lura da hadarin da ke ciki ainun idan aka dora wani ba Kwasau ba a kan gadon mulki, tun da ya san yadda yakin basasa ta kaya a kano, sai kurum ya dora Madaki Kwasau sarautar Zazzau.
Yin haka ke da wuya sai wasu daga mabiya da garuruwa suka fara yin bore.
Sarki Kwasau ya shirya yaki ya tafi Gwari da Kataf da Kadara tare da tilasta musu yin biyayya a gare shi.
Abu na biyu kuma da ya sake raunana Zazzau shi ne, hare-haren da take samu daga wasu sarakunan Hausa, misalin Maradawa da kuma Ningawa.
Idan dai ba a manta ba, a lokacin Maradawa na tsaka da kai hare-hare kasar Hausa. Bayan sarkin su Dan Baskore ya mutu, sai wanda ya gaje shi mai suna Baratiya ya dora a kan inda ya tsaya.
Baya da nan, sai mutanen Ningi, wadanda akai-akai suke kawo hari ga birnin Zazzau. Shi ne har aka ce sun taba yi wa Zazzau din ruwan kibiyoyi a lokacin da suka kawo fada Zazzagawa suka shige cikin ganuwa suka kulle kansu. Kuma har sun kwace ikon wasu garuruwa irinsu Soba, Dutsen Wai da Kubau daga Zazzau.
Kari a kan haka shi ne, sarkin Kwantagora Nagwamutse, shi ma a lokacin ya addabi Zazzagawa da hari.
Duk kuma a wannan lokaci Turawa fakare su kai suna kallon Zazzau. Saboda an ce sun gama lissafa cewar ita ce cibiyar da za ta fi a gare su wajen kafa sansani kafin kai wa Kano da Sakkwato hari.
Kuma kasancewar akwai Turawan mishan da ke gudanar da al’amuransu a Zariya, sai ya zamana Turawa ba su da burki gare ta, suna shigowa su yi hurkokinsu babu tsangwama.
Ana haka, sai labari ya zowa sarkin Zazzau Kwasau cewa, Turawan mishan sun nemi wurin zama a Kano amma Sarki Alu ya kore su, sannan rundunar dakarun Turawa mai suna ‘West African Frontier Force’ (WAFF)’ ta kone garuruwan Remo da Kaje dake karkashin Zazzau, kuma da rade-raden za su kawo wa Zariya yaki don hana cinikin bayi. Sai kawai Sarki Kwasau shi ma ya kori Turawan mishan daga kasar sa suka koma Girku da zama.
Yin wannan ke da wuya sai shugaban waccan runduna ta Turawa mai suna Kaftin Kambell ya kawo ziyara ga Sarki Kwasau, ya ce, ya zo kulla abota ne da shi tare da samar da yarjejiniyar zaman lafiya a tsakaninsu.
Abin da ya kara kwantar wa da Sarki Kwasau hankali a game da Turawa shi ne, yadda suka kame kwantagora tare da korar sarkinsu abokin hamayyarsa Sarki Ibrahim Nagwamutse a shekarar 1901, sannan kuma suka kame sarkin a wani fada da su ka yi a Maska suka aike da shi garin Lokoja aka tsare.
Wannan ya sa hankalinsa ya kwanta da su domin sun yi masa maganin abokin hamayyarsa, suka rinka kwararowa cikin Zariya suna lamurorinsu.
Sai dai kwatsam babu aune, sai sarkin Zazzau Kwasau ya ji Turawa sun ayyana Zariya a matsayin garin da suke iko da shi tare da kawo wani Bature mai suna Kaptin Abadie da aka fi sani da suna Mai jimina a matsayin shugaban na garin, wannan ya sa sarkin cikin damuwa da bacin rai.
Ya shiga tunanin mafita a wannan lamari, gashi yana da rauni wajen fada da Turawa, sannan sarkin Bidda ya aiko masa da gargadin ka da ya kuskura ya ce zai buga da su, gashi kuma yana jin kaskancine ya ci gaba da zama a kasansu.
Don haka mafitarsa biyu ce, ko dai ya hakura ya zauna cikin kaskanci, ko kuma ya nemi taimakon sarkin Kano Alu ya yi yaki da su.
Da tunani ya yi zurfi, sai kurum ya zabi shawara ta biyu.
Sarkin Zazzau Kwasau ya gamsar da zuciyarsa cewa ko kadan ba zai yi biyayya ga Turawa ba, tun da kasarsace ba tasu ba. Kuma ba addini daya gare suba. Don haka ya soma tunanin mafita.
A kan haka ya aike wa Sarkin Kano Aliyu babbar wasikar neman tallafi, yana mai shaida masa cewar Kiristoci sun yawaita a Zazzau, har kuma sun yi kaka gida tare da kokarin mallakinsu, don haka yana neman mafita.
Ana haka, sai rikicin kisan Kyaftin Moloney ya bijiro.
Shi Kyaftin Moloney, shi ne shugaban na Kyaffi. Ita kuwa Kyaffi tana karkashin daular Zazzau ne a lokacin. Kuma Sunan shugabanta wanda yake a matsayin wakilin sarkin Zazzau a Kyaffi shi ne Magaji Dan Yamusa.
Aka ce rannan Kyaftin Moloney ya tara mutane yana musu jawabi, yana karanto turanci gare su, wani bakin mutum kuma yana tafintan abin da duk ya fada.
Magaji Dan Yamusa da tarin wasu jama’a duk suna wurin.
Kwatsam sai rashin fahimta ya dabaibaye tafintan kyaftin Moloney sakamakon tsauraran kalmomin turancin da Moloney ke karantawa, shi kuma tafinta sai ya rinka yi wa turancin fassarar kalma da kalma.
A kan haka ya fada wa mutane cewar Turawa ke da iko da su da komai nasu. Har matayensu ma mallakin Turawa ne.
An ce kafin a ankara sai ganin kan Kyaftin Moloney aka yi yana mirginawa a kasa, Magaji Dan Yamusa ya saro shi.
Daga nan fada ya barke tsakanin mutanen Magaji da dakarun Moloney.
Daga karshe dai, Magaji Dan Yamusa ya gudu da tawagarsa zuwa Kano. Sarkin Kano Alu Babba ya ji dadin abin da bakonsa ya yi, ya karrama shi tare da ba shi mafaka.
Duk da cewar akwai sabanin inda wannan rikici ya auku, shin a Keffi ne ko a Zariya, amma dai Turawa sun dora alhakin faruwar hakan a kan daular Zazzau, tun da a cikin ikon ta abin ya faru.
Sannan kuma sun damu matuka bisa abin da sarkin Kano ya yi, wannan ya sa suka sake daura aniya da kaimin tafiya Kano da yaki duk da cewa daman fakonta suke yi.
Ganin haka sai Sarki Kwasau ya soma shirin guduwa, saboda ya tabbatar abin da zai faru ba mai karewa ba ne.
Ya sake aike wa da wasika ga Sarki Alu babba na Kano, yana sanar masa da cewar lallai ba suga ta zama ba, hadari gagarumi na zuwa gare su.
Su kuwa Turawa sai suka ji tsoron idan sarkin Zazzau ya gudu da mutanensa, to fa zai je ya hadu ne da sarkin Kano su kara karfi, don haka sai suka baza dakarunsu a kan hanyoyin Zariya zuwa Kano, Zariya zuwa Katsina da kuma Zariya zuwa Bauchi, da niyar hana sarkin gudu ko kuma a kame shi idan ya gudo.
Rannan sai kurum kyaftin Abadie, ya aike wa Sarki Kwasau gayyata domin tattaunawa.
Sarki Kwasau ya fusata da haka, ya ce don me kamar kyaftin Abadie Kirista da yake a kasarsa zai kira shi ya zo, don haka ba zai je ba.
Daga nan sai Turawa suka samu yadda suke so, suka turo dakaru masu dimbin yawa cikin Zariya, suka yi wa fadar Sarki kwasau kawanya, sannan suka shiga suka kama shi tare tafiya da shi Wushishi. A can suka tsare shi har Allah ya yi masa rasuwa.
Kuma an samu cewar Sarki Kwasau ya yi rubututtuka dangane da yadda aka kamashi da halin da ya tsinci kansa. A ciki akwai wata takarda mai suna ‘Nuzhatul Asiyr’ inda ya rubuta cewar Turawa sun kama shi ne bisa kin yi musu biyayya, a yammacin wata ranar jumu’a cikin kwanaki goman karshe na watan Jumada Ula. (dai-dai da 19- Satumba-1902).
Sannan kuma ya bayyana farin cikinsa bisa yadda suka kama shi ba tare da ya bi umarnin su ba ya zauna aka karkashinsu, har ma ya kamanta kansa da mutanen Ashabul Kahfi.
Daga karshe, sai Turawa suka nada Galadima Salmanu sarkin Zazzau a farkon shekarar 1903.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!