Connect with us

LABARAI

Dalilin Da Ya Sa Ba Ni Da Gidan Kaina – Dangote

Published

on

Mutumin da ya fi arziki a Afrika, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ba shi da wani gida a waje ko cikin Najeriya. Dangote ya nuna cewa, ya guje wa abubuwa masu ban sha’awa, jin dadi da sharholiya “saboda su na jan hankali kuma su na daukar lokaci” ne.
Dangote ya ce: “Ba ni da gidan hutu a ko’ina. Ba ni da gida a ko’ina amma na san mutanen da suke aiki a gare ni suna da gida a London. “
“Amma kuna gani, mutane da yawa, har ma da matasan, muna bukatar mu yi hankali saboda daya daga cikin manyan matsalolin da muke da shi a matsayin ‘yan Afrika shine cewa muna ciyar da sakamakonmu na kudi.
“Da zarar ka fara yin kasuwanci kuma yana fara aiki da kyau, amma maimakon ka zuba jari a cikin kasuwancin, ka fara yin tunanin cewa riba zai ci gaba da zuwa.
“Akwai matsala da kuma raguwa a kasuwanni don haka dole ne ku mai da hankali sosai.”
Da aka tambaye shi game da yankunan da matasan ‘yan kasuwa suke zuba jari, Dangote ya amsa ya ce: “Yankunan da za su mayar da hankali ga yanzu shine Abuja da aikin noma. Wadannan su ne bangarori biyu masu ba da gudummawa. “
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!