Connect with us

KASASHEN WAJE

Pompeo Ya Zargi Chana Da Satar Fasahohin Yankin Kudancin Amurka

Published

on

Irin harkokin kasuwancin da China ke yi a yankin Kudancin Amurka, na da babbar alaka da manufofin tsaron Kasarta da burinsu na bunkasa fannin kere-kerensu zamani da kuma satar fasahohi.”
Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya ce al’umar Kasar Benezuela ta dawo daga rakiyar Shugaba Nicolas Maduro da gwamnatinsa.
Yayin wata hira da ya yi da ‘yan jaridu, a lokacin ziyarar da ya kai Kasar Paraguay a jiya, babban jami’in diplomasiyyan na Amurka, ya ce, zaben da Shugaba Maduro ya ce lashe, zabe ne da aka tafka magudi.
Pompeo ya kara da cewa, Kasashen duniya 54, sun amince da jagoran ‘yan adawa Juan Guido, a matsayin Shugaban wucin gadi na Kasar ta Benezuela.
Ya kuma zargi Maduro da yin amfani da Rasha da Cuba da kuma Chana, wacce ya ce tana bai wa jami’an Kasashen yankin kudancin Amurka cin hanci domin samun biyan bukatun kanta.
Ya ce “Irin harkokin kasuwancin da Chana ke yi a yankin Kudancin Amurka, na da babbar alaka da manufofin tsaron Kasarta da burinsu na bunkasa fannin kere-kerensu na zamani da kuma satar fasahohi.”
Pompeo ya kara da cewa, Amurka na da burinta ga Chana ta ci gaba, amma ba ta bin wannan tafarki ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!