Connect with us

LABARAI

Shugabancin Majalisun kasa: Gwamnonin APC Sun Amince Wa Lawan Da Gbajabiamila

Published

on

Gwamna Kashim Shettima, na Jihar Borno ya ce, tsaffin gwamnonin jam’iyyar APC da suke cikin majalisun kasa a zama na 9, sun amince da takaran Sanata Ahmed Lawan, a matsayin shugaban majalisar Dattijai.

Shettima, ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a kan hakan, a  birnin N’Djamena, na kasar Chadi, ya kara da cewa, hakanan, zababbun ‘yan majalisun kuma sun amince da takaran Femi Gabaijamila, a matsayin Kakakin majalisar wakilai ta kasa.

Gwamnan kuma ya bayyana cewa, duk Sanatocin da aka zaba din da kuma wakilan majalisar ta wakilai a matakin tarayya daga Jihar ta Borno, sun amince da takaran Lawan da Gbajabiamila.

Don haka, sai ya yi watsi da rade-radin da wasu ke yi na cewa tsaffin gwamnonin da suke a majalisun kasan suna kalubalantar zaben na Lawan da Gbajabiamila, a matsayin shugabannin majalisun biyu na tarayya.

A cewar Shettima, hanya guda da gwamnonin na APC za su nuna godiyar su ga Shugaba Buhari, ita ce na su goya wa duk wasu shiye-shirye na shi baya, da kuma shawarar sa da ya zartar na siyasa.

“Duk Gwamnonin mu, har ma da sabbin masu shigowa majalisar ta dattijai, duk suna goyon bayan matakin da jam’iyyarmu ta dauka a kan zaben shugabannin majalisun biyu.

“In har za a bar kowa ya yi zaben a bisa son ransa ne, tabbas za a sami matsala da rashin fahimta.

“Don haka, muka alakanta kanmu da duk abin da shugaban kasa ya karkata a kansa,” in ji shi.

Gwamnan wanda yana daga cikin tawagar shugaban kasan da suka yi wa shugaban kasan rakiya domin saduwa da sauran shugabannin kasashen na yankin Sahel, a birnin na N’Djamina, ya bayyana fatan da yake da shi, na cewa taron shugabannin zai fitar da mafita a kan matsalolin tsaro da ke addaban yankin.

Ya kuma yabawa shugaba Buhari, a kan irin rawar da yake takawa wajen neman samun zaman lafiya da daidaito a yankin, gwamnan ya bukaci sauran shugabannnin yankin da su karfafa goyon bayan su wajen magance matsalolin tsaro da ta’addanci da suke fuskantar yankin na tafkin Chadi da ma bayansa.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!