Connect with us

LABARAI

 An Kama Mutum Hudu Da A ke Zargi Da Tsafi  A Ribas

Published

on

Jamián tsaron jihar Ribas, sun kama mutum hudu da ake zargin suna cikin kungiyar asiri a Rumuolumeni, dake karamar hukumar Obio/Akpor a jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan Sandan, DSP Nnamdi Omoni, shi ne ya bayyana hakan a yau Litinin a garin Fatakwal.

Ya ce; wadanda ake zargin cewa suna cikin kungiyar asirin an kame su ne a wani samame da jami’ansu na sashen Rumuolumeni suka kai a ranar 18 ga watan Afrilu. A cewarsa sun yi wannan kamen ne a wani matakin kawo karshen masu kungiyar asirin a jihar.

Ya ci gaba da cewa; an kama su da karamar bindiga da kuma kwansan harsasai sannan sun tabbatar da zargin da ake musu. Ya ci gaba da cewa; za su ci gaba da kai samamen domin ganin sun kama sauran wadanda ake zargi da irin wannan harkar. Kuma ya tabbatar da cewa za su kais u kotun domin ganin an yanke musu hukunci.

Har wala yau rundunar ‘yan Sandan sun ce za su tabbatar da sun kawo karshen ‘yan bindiga a jihar, amma a cewarsu hakan ba zai yiwu ba sai da taimakon al’umma. Inda ya roki al’umma da su taimaka musu da rahotannin duk abin da ba su yarda da shi bag a ‘yan Sandan ta wadannan nambobi; 08033312261, 08033396638 da 08098880134.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!