Connect with us

WASANNI

Ramsey, Petr Cech Da Welbeck Sun Yi Bankwana Da Arsenal

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Aaron Ramsey, ya fashe da kuka bayan da yayi bankwana da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kuma ya kawo karshen zamansa a kungiyar bayan ya shafe shekara 11 yana bugawa kungiyar wasa.
Ramsey, wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a shekara ta 2008 lokacin tsohon kociyan kungiyar Arsene Wenger daga kungiyar Cardiff City ya buga wasanni da dama a kungiyar kuma ya lashe kofin FA Cup guda biyu a jere a kungiyar.
Ramsey, mai shekara 28 a duniya ya kasance dan wasan tsakiyar da yafi kowanne dan wasan tsakiya a kungiyar cin kwallaye bayan ya zura kwallaye 36 cikin wasanni 228 daya bugawa kungiyar tun daga shekara ta 2011 zuwa yanzu.
“Ba zan iya jurewa ba domin shekara 11 ba wasa ba ce a kungiya daya kuma zan kasance ina kewar wanann kungiya a rayuwata wadda tayi min komai tun ina matashin yaro har na zama mutum nayi aure na tara iyali kuma na kafa tarihi” in ji Ramsey dan kasar Wales.
Ya cigaba da cewa “Arsenal kungiya ce wadda ta zama komai a rayuwasa sai dai lokaci yayi da zan bar kungiyar in koma kungiyar da zan cigaba da buga wasa da dan wasa Cristiano Ronaldo kuma zan buga kofin zakarun turai”
Shi ma mai tsaron ragar kungiyar, Petr Cech, wanda ya koma kungiyar a shekarun baya ya kawo karshen zamansa a kungiyar a wannan kakar bayan da shima yayi sallama da magoya bayan kungiyar a filin wasa na Fly Emirates kafin a fara wasan da kungiyar ta buga 1-1 da kungiyar Brighton Albion.
Haka shi ma dan wasa Danny Welbeck, wanda ya koma kungiyar a shekara ta 2014 daga kungiyar kwallon kafa ta Manchester United yayi sallama da magoya bayan kungiyar bayan da kungiyar ta tabbatar da cewa bazata kara masa sabon kwantaragi ba kuma ya buga wasanni 126 a kungiyar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!