Connect with us

KASUWANCI

Sabon Albashi Ba Zai Haifar Da Hauhawar Farashi Ba – Masanin Tattalin Arziki

Published

on

Wani kwararre a fannin tattalun arziki Farfesa. Uche Uwaleke ya yi nuni da cewar, sabon karin albashi na naira 3,000 ba zai janyo hauhawan farashi ba sabanin yadda wasu yan Nijeriya suke yin yamadin cewar karin zai janyo hauhawan farashin.
Uwaleke, wanda kuma Shugaba ne na sashen koyon aikin banki da hada-hadar kudi a jami’ar jihar, Nasarawa da ke Keffi, ya sanar da hakan ne a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa babban birnin tarayyar Abuja.
A cewar Farfesa Uche Uwaleke , “ Sam ni ban yarda cewar sabon albashin zai haifar da hauhawan farashi ba domin har yanzu bukatun da muke dashi yanada rauni.”
Ya yi nuni da cewar, “ kangin tantalin arzikin kasa domin bukatar tanada rauni saboda gwamnatocin jihohi da dama bazasu iya biyan albashin ma’aikatansu ba saboda ragin da aka samu na abinda aka basu na farashin mai.”
Ya kara da cewa,“ tattalin arzikin kasa yana farfadowane a hankali tun bayan da Nijeriya ta fice daga kangin tattalin arzikin kasa.”
Farfesa Uwaleke ya buga misali da rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta fitar na wata ya nuna cewar, huhawan farashi yana tafiya kafada da kafada da ayyukan tattalin arzikin kasa.
A cewarsa, wannan yana faruwa ne saboda da tsadar farashin man fetur, wutar lantarki da kuma sufuri.
Ya kara da cewa, tarihi a bayyane ya nuna cewar karin albashi bazai janyo hauhawan farashin kayan masarufi ba.
A cewarsa, “a shekarar 2011 alal misali, a lokacin da akayi karin sabon albashi daga naira 7,500 zuwa naira 18,000, hauhawan farashin ya ragu daga sama da kashi 13 bisa dari a shekarar data gabata kasa da kashi 11 bisa dari.
Kudurin sabon karin na mafi karancin albashin na naira 30,000 Majalisar kasa a ranar 29 na wata Janairi da kuma ranar 19 ga watan Maris suka amince dashi, inda kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 18 ga watan Afirilu ya rabbata masa hannu ya zamo doka.
Kamfanin dillancin labarai na kasa, ya ruwaito cewar, kwararrun a fannin tattalin arziki da dama sunyi jayayyar akan cewar, wanzar da sabon karin albashin zai haifar da hauhawan farashi a cikin Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!