Connect with us

WASANNI

Yakamata Chelsea Ta Dinga Buga Kofin Zakarun Turai Duk Shekara – Hazard

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Edin Hazard, ya bayyana cewa daman duk shekara yakamata ace kungiyar Chelsea tana buga gasar cin kofin zakarun turai saboda gogayya da manya manyan kungiyoyi.
Chelsea na daf da samun gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta Champions League ta badi, bayan da ta doke kungiyar kwallon kafa ta Watford 3-0 a ranar Lahadi a wasan karawar mako na 37, ta ci kwallaye ta hannun Ruben Loftus-Cheek da Dabid Luiz da kuma Gonzalo Higuain.
Da wannan sakamakon Chelsea ta koma ta ukun teburi, bayan da a ranar Asabar Bournemouth ta doke Tottenham 1-0 kuma Chelsea za ta kammala firimiya bana a mataki ta ukun teburi idan ta yi nasara a wasan karshe da za ta ziyarci Leicester City ranar Lahadi mai zuwa.
“Kowa ya san Chelsea babbar kungiya ce kamar manyan kungiyoyin duniya saboda tana da tarihin lashe kofin zakarun turai saboda haka daman ya kamata ace koda yaushe suna buga gasar domin abinda yakamata ace tana bugawa kenan” in ji Hazard, wanda ake saran zai koma Real Madrid.
Canjaras ma zai iya sa Chelsea ta kare cikin ‘yan hudun farko a teburin shekarar nan, amma hakan zai dogara kan sakamakon wasannin karshe da za a rufe kakar bana har ila yau kuma Chelsea tana buga gasar Zakarun Turai ta Europa, inda ta je ta tashi 1-1 a gidan Frankfurt a makon jiya, kuma za ta karbi bakuncin wasa na biyu ranar Alhamis mai zuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!