Connect with us

WASANNI

Najeriya Ta Bayyana Sunayen ’Yan Wasan Da Za Su Wakilce Ta A Kofin Duniya

Published

on

Tawagar ‘yan wasan Najeriya na ‘yan kasa da shekara 20 ta sanar da sunayen ‘yan wasan da zasu bugawa kasar wasa a gasar cin kofin duniya wanda kasar Poland zata karbi bakunci a wata mai kamawa yayinda dan wasan Manchester City, Tom-Dele Bashiru ya samu shiga cikin ‘yan wasan.

Wannan ne karo na 12 da kasar nan zata samu halartar gasar sai dai dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist ta garin Bauchi, Adeshina Gata, bai samu damar shiga cikin ‘yan wasan da aka gayyata ba.

Najeriya dai ta fito acikin rukuni na D daya hada da kasashen Katar, da Ukraine da kuma kasar Amurka yayinda ‘yan wasan na Najeriya zasu fara buga wasa da kasar Katar a ranar 24 ga wannan watan.

Ga Sunaye ‘Yan Wasan Da Aka Gayyata Da Kungiyoyinsu:

Masu Tsaron Raga: Detan Ogundare (Kogi United); Olawale Oremade (Kwara United; Jonathan Zaccala (Triestina FC, Italiya)

’Yan Wasan Baya: Balentine Ozornwafor (Enyimba FC); Aliu Salawudeen (Amuneke Academy); Igoh Ogbu (Rosenborg BK, Norway); Ikouwem Utin (Enyimba FC); Muhammad Rabiu (Plateau United); Jamil Muhammad (Kano Pillars)

’Yan Wasan Tsakiya: Nnamdi Ofoborh (AFC Bournemouth, England); Eletu Peter (Prince Kazeem FC); Ayotomiwa Dele-Bashiru (Manchester City, England); Kingsley Michael (AC Perugia, Italy); Effiom Madwell (Enyimba FC); Aniekeme Okon (Akwa United); Collins Sor (Oasis FC)

’Yan Wasan Gaba: Jerome Adams (Sogndal IL, Norway); Tijani Muhammed (FC Banik Ostraba, Czech Republic); Henry Offia (IK Sirius Uppsala, Sweden); Chinonso Emeka (Club Brookhouse, England); Success Makanjuola (Water FC)
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!