Connect with us

MANYAN LABARAI

PDP Na Yunkurin Kifar Da Gwamnatin Buhari –Gwamnatin Tarayya

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta yi zargin wani yunkurin bita-da-kulli da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar, da ma jam’iyyar PDP din ta kasa, suke yi wa gwamnatin Shugaban Kasa Buhari. Gwamnatin Tarayya ta gargadi Atikun da jam’iyyar PDP su sake takun su, ko su fuskanci tuhumar yi wa kasa zagon kasa.

Ministan watsa labarai, Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana wa manema labarai hakan yau Laraba a fadar gwamnatin tarayya. Lai ya ce; ba daidai bane matakin da PDP da dan takarar ta suke shirin dauka ba, maimakon su rungumi kaddara bayan da suka fadi a zabe, sai suke so su yi amfani da wannan damar wajen yi wa gwamnati zagon kasa.

Ministan ya zarge PDP da dan takarar ta da furta wasu kalamai da suka fi kama da yi wa kasa bita-da-kulli, inda ya bada misalin wata magana da Atiku ya ta furta, cewa; in har ‘yan Nijeriya ba su yaki APC ba, to kashe-kashe ba zai yi sauki ba a kasar.

‘Gwamnatin tarayya ta na Allah-wadai da ayyukan da wasu marasa kishin kasa su ke yi, musamman ma dai abinda jam’iyyar PDP ta ke yi, akwai hatsari in har ba a tsayar da wannan lamarin ba, don haka muke mu su gargadi.’ inji Lai
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!