Connect with us

WASANNI

PSG Za Ta Sayi ’Yan Wasa Uku Daga Real Madrid

Published

on

Rahotanni daga kasar Faransa sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German tana shirin farwa Real Madrid domin siyan ‘yan wasanta guda uku da suka hada da Gareth Bale da Toni Kroos da kuma Isco.

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai, Zidane, ya bayyana cewa ya gama yanke shawara akan dan wasa Gareth Bale saboda bazai yi amfani dashi ba a kakar wasa mai zuwa wanda hakan yasa baiyi amfani dashi ba a wasanni biyu da kungiyar ta buga a baya.

Bale dai ana ganin karshen zamansa yazo a Real Madrid bayan da Zidane yaki saka sunansa acikin ‘yan wasa 18 na kungiyar a wasanni biyun da kungiyar ta buga  a baya kuma tuni wakilin dan wasan yayi fatali da abinda Zidane yake yiwa dan wasan.

Sai dai shima dan wasa Toni Kroos, wanda ya koma kungiyar daga kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ana ganin zamansa yazo karshe a kungiyar wanda hakan yasa kungiyoyi da dama suka fara zawarcinsa ciki har da Manchester United da PSG din.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, PSG tana son siyan ‘yan wasa Gareth Bale da Toni Kroos domin su koma kungiyar yayinda shima dan wasa Isco, dan kasar Sipaniya yake kokarin barin Real Madrid sakamakon rashin jituwa da shugabannin kungiyar.

An bayyana cewa gaba daya ‘yan wasan guda uku kudinsu zai kai fam miliyan 180 wanda hakan yasa PSG din take ganin idan tayi kokari zata samesu kuma har ila yau kungiyar tana zawarcin dan wasan Lille, Nicolas Pepe wanda shima PSG din take nema ruwa a jallo.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!