Connect with us

WASANNI

Zan Buga Kofin Afrika, Cewar Mikel Obi

Published

on

Dan wasan tsakiyar tawagar ‘yan wasan Najeriya, John Obi Mikel, ya bayyana cewa zai wakilci kasar nan a gasar cin kofin nahiyar Africa da kasar Masar zata karbi bakunci a wata mai kamawa bayan ya dauki tsawon lokaci bai bugawa kasar wasa ba.

Obi, wanda rabon daya bugawa Najeriya wasa tun a gasar cin kofin duniya da aka fitar da kasar nan a wasannin cikin rukuni a kasar Rasha kuma bai bugawa Najeriya wasanni bakwai ba data buga a kwanakin baya ciki har da wasanni biyar na neman cancantar shiga kofin na Africa.

Bayan wata tattaunawa da kociyan Najeriya, Gernot Rohr, Obi, mai shekara 32 a duniya ya bayyana cewa a shirye yake daya sake saka rigar Najeriya domin ya wakilce ta a gasar cin kofin na Africa na wannan shekarar.

“Munyi Magana da Gernot Rohr, kuma ya gayamin shirye shiryensa da yake yi domin tunkarar gasar cin kofin nahiyar africa kuma nayi farin ciki da hakan kuma nima zan kasance a gasar idan lokaci yayi” in ji Mikel Obi.\

Mikel Obi dai kawo yanzu yana bugawa kungiyar kwallon kafa ta Middlesborough wasa a kasar Ingila kuma ya koma kungiyar ne a watan Janairun daya gabata sai dai duk da cewa yayi kokari a kungiyar amma basu samu damar komawa gasar firimiya ba ta bana.

Yanzu dai Obi zai mayar da hankali wajen ganin Najeriya ta samu nasarar lashe gasar ta Africa karo na hudu kuma Najeriya ta fito acikin rukuni na B daya hada da kasashen Madagascar da Burundi da kuma kasar Guinea.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!