Connect with us

Da dimi-diminsa

Kotu Ta Bada Umurnin A Kamo Hadiza Gabon

Published

on

Labarin da ke shigowa jaridar LEADERSHIP A Yau ya tabbatar da cewa wata Kotun Majistari da ke zama a Birnin Kano, karkashin jagorancin Alkali Muntari Gambo Dandago, ta umurci Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano da ya kamo mata Jarumar Fim din hausa, Hadiza Gabon.

Sannan kuma kotun ta umurci kwamishinan ‘yan sandan da ya binciki zargin da mai kara, Jarumi Mustapha Naburaska ya shigar a kan zargin cin zarafinsa da Hadiza Gabon din ta yi.

Alkalin ya yanke wannan hukunci ne sakamakon kauracewa zaman kotu da Hadiza Gabon ta yi a yau Alhamis.

Idan dai ba a manta ba, tun a kwanakin baya ne Naburaska ya shigar da karar Gabon kan zargin cin zarafi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!