Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Haramta Nadin Sabbin Sarakunan Jihar Kano

Published

on

•Ba A Fahimci Hukuncin Ba – Gwamnatin Kano
Wata babbar Kotu a Kano da ke zamanta a Ungogo a jiya Laraba ta bayyana nadin da aka yiwa sabbin Sarakunan nan hudu da Gwamnatin Jihar Kano ta yi a matsayin haramtattu. Da ya ke yanke hukuncin a ranar Laraba, Mai shari’a Nasiru Saminu, ya umarci dukkanin bangarorin da a ka ambata a cikin karar da su tabbata a matsayin da ake kai na 10 ga watan Mayu har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren korafin da kuma gabatar da hukuncin Kotu a kan al’amarin.
Idan ba a manta ba, a rahoton da ya gabata na ranar goma ga watan Mayun shekarar 2019, Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da umarnin Kotu tare ci gaba da bayar da takardun kama aiki ga sabbin sarakunan. Haka zalika, a tsakanin ranakun 11 da 12, Gwamnan Kanon ya sake tabbatar da raba takardun kama aiki ga Sarakunan hudu.
Har ila yau, jim kadan bayan bayyana wannan rahoto na kotu, mai magana da yawun fadar Gwamnatin Kano, Malam Abba anwar ya karyata wancan batu na cewa, Kotu ta haramta nadin sabbin Sarakuna hudu a Kano.
A jiya ne mai Magana da yawun Fadar Jihar Kano, ya bayyana wa manema labarai cewa, batun soke sababbin Masarautun Kanon, ba gaskiya ba ne kawai shaci fadi ne.
“Labarin da Jaridar nan mai adawa da gwamnatin jihar Kano, wato Daily Nigerian ta fito da shi a jiya cewa, wai Kotu ta sauke sabbin Sarakunan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nada bisa doka kwanan nan, labarin kanzon kurege ne.
Kawai dai ana so a kara kawo rudani ne a wannan ci gaban da aka samu a jihar ta Kano. Kuma ai ita waccan Jaridar dama kowa ma ya san irin kallon da ta ke yiwa wannan gwamnati tamu, musamman a bangaren yarfe da kage da fadar abinda bai tabbata a kan wannan gwamnati ba,” in ji Anwar.
Ya ci gaba da cewa, wani abin lura a nan shi ne yadda waccan Jarida ta yi kaurin suna wajen adawa ta ba gaira ba dalili ga gwamna Ganduje da gwamnatinsa. Wannan labarin wai na sauke Sarakunan Bichi da Rano da Gaya da Karaye, ba haka zancen ya ke ba sam. Ita waccan babbar Kotun da ke zamanta a Ungogo karkashin mai Shari’a, Nasiru Saminu cewa kawai ta yi, kowa ya je ya tsaya a matsayin da ya ke, in ji shi.
“To mu a nan Jihar Kano, tun daga lokacin da Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta kawo kudirin Doka wacce Gwamna Ganduje ya sanya wa hannu ta zama Doka, zuwa lokacin da aka baiwa wadannan sababbin Sarakuna takardar shaida na wannan zabe da aka yi musu har zuwa lokacin da aka ba su sandar mulki, Gwamnan Kano bai karbi wata Oda daga Kotu cewa, ya dakata da yin nadin nasu ba.
Kadai abin da mai Shari’a ya ce, kowa ya tsaya matsayinsa har sai lokacin da za a fara sauraren wancan koke da aka kai masa. An kuma sanya ranar 21 ga Watan Yunin, 2019 mai zuwa a matsayin ranar da za a fara sauraren karar. Mu kuma a matsayin da muke a halin yanzu shi ne, mun nada wadancan Sarakuna masu daraja ta daya tun ma kafin a ce wai an ba wa Gwamna wata Oda sabanin hakan”, in ji babban Sakataren yada labarai na Gwamnan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!