Connect with us

KASUWANCI

Sama Da Naira Tiriliyan 30 Suka Shiga Asusun TSA Cikin Shekaru Hudu

Published

on

Tun lokacin da aka wanzar da Asusun bai daya na TSA daga shekarar 2015 zuwa yau, kimanin naira tiriliyan 30 suka shiga cikin Asusun. Wannan naira tiriliya 30, ta hadada, wanda aka biya da kuma wanda aka cire daga cikin Asusun na TSA.

Wani jami’i

Mista Sylba Okolieaboh , wanda Darakta ne kuma jami’ dake kula da shigar da kudade a cikin Asusu ya sanar da hakan a ranar Talatar data gabata a hirar sa da wakilin Jaridar Daily Trust a lokacin da tawagar wasu wakilai daga kasar Gambiya suka ziyarci Ma’aikatar kudi ta tarayya dake babban birnin tarayar Abuja don neman ilimi akan yadda Gwamnatin Tarayya take tafiyar da Asusun ta na TSA.

Acewar Mista Sylba Okolieaboh, “ Idan kuna kallo ne a bisa hada-hadar kudi, mun samu ribar data kai ta naira tiriliyan 30 , sai dai, kada ku manta wadanan kudaden suna shiga ne suna kuma fita.’’

Mista Sylba Okolieaboh ya ci gaba da cewa, tsarin Asusun TSA na Nijeriya an samu gagarumar cin nasara, inda har hakan ya sanya wasu kasashe suke nuna sha’awar su zuwa Nijeriya don suyi koyi da tsarin.

Darakta Mista Sylba Okolieaboh ya kara da cewa, “ Munyi namijin kokari sosai akan Asusu mu na TSA kuma muna jin dadi akan yadda ita kanta duniya ta gamsu da hakan.”

Mista Sylba Okolieaboh ya yi nuni da cewar,” kasar Gambiya tazo muna kuma jiran kasar Habasha da sauran kasashe others.”

Acewar Mista Sylba Oolieaboh tsarin Asun na TSA yana da matukar mahimmanci ga tafiyar da tattalin arzikkn kasa, inda ya kara da cewa, ya kasance yana daya daga cikin wadanda suka gudanar da sauye-sauye na fanin kudi a kasar nan a tsawon lokutan da suka gabata, amma bai ga inda akafi samun cin nasara a cikin sauri ba sai a tsarin Asusun TSA na kasar nan.

Mista Sylba Okolieaboh ya sanar da cewar, an samu wannan cin nasarar ce a cikin dan lokaci kuma kusan kowan ya shiga tsarin, musamman ganinn yadda aka samar da daidaito.

Ya sanar da cewar, ko kusa ba’a yarda an sanya siyasa a tsarin ba.

A karshe Mista Sylba Okolieaboh yace, dukkam wannan nasarar ta samu ne saboda jajircewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannin.˙
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!