Connect with us

KASUWANCI

’Yan Nijeriya Sun Samu Kwangilar Dala Miliyan 368 A Matatar Man Dangote

Published

on

Matatar Man Dangote ta baiwa ta baiwa yan kwangila dake cikin Nijeriya su 120 kwangilar kimanin dala miliyan 368 a matatar man dake a jihar Legas.

Matatar tayi hakan ne a karkashin shirin ta na inganta yin amfani da kayan gida.

Mista Debakumar Edwin, Daraktan tsare-tsare, samar da ci gaba da gudanar da manyan ayyuka na Masana’antar Dangote ne ya sanar da hakan a ranar Talatar data gabata a jihar Legas.

Mista Debakumar Edwin wanda ya sanar da hakan a lokacin da yake zagayawa da yayan kungiyar yan jarida reshen jihar Legas da kuma Cibiyar dake hudda da jama’a NIPR yaci gaba da cewa, akwai kayan cikin gida da za’a iya yin amfani dasu a matatar man ta Dangote.

Acewar Mista Debakumar Edwin, akwai dimbin kayan cikin gida masu yawa a Nijeriya da matatar man ta Dangote zata iya amafana dasu, musamman wajen yin amfani da fasahar zamani da kuma kwarewa.

Yace, an gina matatar man ta Dangote ne a bisa kwarewa da kuma samar da ci gaba, inda ya sanar da cewa, tuni kamfanin na Dangote ya yi hadaka da Gwamnatin jihar Legas da kuma kamfanin Siemens don daukaka kwarewa da samar da ci gaba a inda aka kafa matatar man ta Dangote a jihar Legas, musamman din a samar da ayyukan yi a matatar man ta Dangote.

Ya sanar da cewa, baya ga daukar yan kwangilar aiki a kwanan baya da kamfanin na Dangote ya yi, kamfanin ya zuwa yanzu, ya kuma dauki yan Nijeriya kimanin su 3,580 a matatar man ta Dangote.

Mista Debakumar Edwin ya sanar da cewa, an kafa matatar man ta Dangote akan Eka 6,180 daidai da kadada 2,500 dake shiyyar Lekki a cikin jihar Lagos.

Acewar Mista Debakumar Edwin, matatar man ta Dangote zata sarrafa kimanin gangunan danyen mai 650,000 a kullum da za’a dinda tura danyen man ta hanyar bututun mai daga filin da ake hakar man a jihar Niger Delta, inda kuma anan ne za’a dinga samo gundarin iskar gas da kuma yin amfani da ita wajen turawa a masana’antar sarrafa takin zamani, tare da yin amfani da ita wajen sarrafa samar da wutar lantarki a matatar man ta Dangote.

A karshe Mista Debakumar Edwin yace, aikin matatar man ta Dangote ana sa ran zai lashe jimlar dala biliyan 15, tare da zuba jarin dala biliyan 10 a matatar man, inda aikin takin zamani a matatar man zai lashe dala biliyan 2.5, aikin sanya bututun mai kuma zai lashe dala biliyan 2.5.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!