Connect with us

MANYAN LABARAI

Kamar Yadda Ta Faru A Zamfara Haka Za Ta Faru A Kano – Abba Kabir Yusif

Published

on

Dan Takarar Gwamnan Kano a tutar Jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusif ya bayyana kyakkyawan fatansa na cewa, Kotun sauraron korafe-korafen zabe za ta kwato musu hakkinsu daga hannun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kamar yadda ta faru a Jihar Zamfara.
Dan takarar ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake mayar da martani kan rushe dukkanin wadanda suke ganin su ne suka lashe zabe a Jihar Zamfara karkashin Jam’iyyar APC da Kotun koli ta yi a ranar Juma’ar da ta gabata.
Kotun daga ke sai Allah ya isan, da sanyin safiyar ranar Juma’a ta yi watsi da bukatar da Jam’iyyar APC ta daukaka kara a gabanta, inda ta ke
kalubalantar Hukumar zabe (INEC) da kin mika shaidar lashe zabe ga Dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC, Muktar Koguna a Jihar ta Zamfara.
A cikin hukuncin da Kotun kolin ta yi, ya bayyana Jam’iyyar ta APC da gaza gudanar da zaben fid da gwani na cikin gida kamar yadda yake a Kundin tsarin mulkin Jam’iyyar. A cikin hukuncin da Mai shari’a Paul Galinji ya yi, ya bayyana cewa kotun kolin ta rushe duk wasu kuri’u da aka kada wa Jam;iyyar ta APC a babban zaben day a gabata na shekarar 2019.
Har ila yau, Dan takarar gwamnan karkashin Jam’iyyar PDP na Kano Abba Kabir Yusif, a shafinsa na Twitter, ya taya Jam’iyyar PDP da sauran al’umma Jihar Zamfara murna bisa wannan gagarumar nasara da suka samu. Haka nan, ya bukaci Kanawa musamman ‘Yan Jam’iyyarsa ta PDP, su kara jajircewa da addu’a domin samun nasarar shari’ar da suka sanya a gaba.
A daidai wannan lokaci da nake taya al’ummar Zamfara murna tare da Abokina Alhaji Bello.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: