Connect with us

KASUWANCI

Kamfanin MTN Ya Tabbatar Da Samamen EFCC A Ofishinsa Na Legas

Published

on

Kamfanin sadarwa na MTN dake gudanar da ayyukan sa a Nijeriya ya tabbatar da cewar, Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma yiwa tattalin arziki Nijeriya zagin kasa EFCC ta kaiwa ofishin kamfanin dake Falomo a yankin Ikoyi a cikin jihar Legas ziyara, don binciken zargin badakalar rubanya shiyar sa da kamfanin ya yi a kasuwar musayar kudi ta kasa NSE.
Lamarin mai yuwa, ya janyo raguwar farashin shiya na kamfanin na MTN dake gudanar da ayyukan sa a Nijeriya, a kari na farko tun bayan da kamfanin ya zuba shiyar sa a kasuwar, takamai mai bayan da kamfanin ya samu kashi 65 bisa dari na naira 59 a cikin sati daya kacal daga naira 90 na ko wacce shiya daya daya ta kamfanin na MTN da akayi hada-hada a kasuwar ta NSE, zuwa naira 149 na ko wacce shiya daya a ranar Alhamis data gabata.
Sai dai, farashin shiya na kamfanin na MTN dake gudanar da aikin sa a Nijeriya ta ragu a karo na farko a ranar Juma’ar data gaba, ganin cewar an rufe akan naira 140 na ko wacce shiya daya.
Jaridar This day ta ruwaito cewar, kasuwar ta SEC a kwanan baya ta kaddamar da gudanar da bincike akan hanyar data kamfanin na MTN dake gudanar da ayyukan sa a Nijeriya akan shiyar da ya zuba a kasuwar ta NSE, duk da cewar, mahukuntan kasuwar sun kare kamfanin.
Amma a cikin sanarwar da Sakataren kamfanin ya rattabawa hannu Mista Uto Ukpanah, da jaridar ta This day ta samo, kamfanin na MTN ya sanar da cewar, Hukumar ta EFCC bata wani zargi kamfanin na MTN da aikata wani laifi ba.
Har ila yau, jaridar ta This day ta ruwaito Hukumar ta EFCC ta kai samame a ofishin na kamfanin na MTN da misalin karfe 4 na yammar ranar Juma’ar data gabata, inda ta kama manyan jami’ai a kamfanin na MTN bayan da jami’an na EFCC suka bukaci wasu muhamman takardu, wadanda a nan take jami’an kamafnain suka mikawa jami’an na EFCC.
Bugu da kari, Jaridar ta This day, ta kuma ruwaito cewar jami’an na EFCC a lokacin ziyarar tassu da suka kai kamfanin na MTN, mahukuntan kamfaninn na MTN da kuma ma’aikatan kamfanin ba’a dsnganta su da zargin ciwa-ciwar shiyar ba ta zuba jarin a kasuwar ta NSE ba.
A cewar sanarwar da Sakataren kamfanin na MTN Ukpanah, kamfanin na MTN dake gudanar da ayyukan sa a Nijeriya ya karbi wasika a ranar 23 ga watan Mayu shekarar 2019 daga gun Hukumar EFCC na bukatar a bata bayanai da kuma takardun da suka shafi zuba shiya da kamfanin ya yi a kasuwar ta NSE.
Sanarwar ta jaddada cewar, Hukumar ta EFCC, bata zargi kamfanin na MTN dake gudanar da aikinsa a Nijeriya da aikata wani laifi ba.
Sanarwar taci gaba da cewa,“Muna son mu kara jaddada cewar, sai da muka bi ka’ida wajen neman amincewar dukkan mahukuntan da suka dace a kasar nan don neman amincewar su munzuba shiyar mu a kasuwar ta NSE kamar yadda itama kasuwar da kanta ta tabbatar da hakan ta hanyar shedawa duniya harda Hukumar dake sanya ido akan musayar kudi ta kasa ta SEC.
Sanarwar taci gaba da cewa, “A matsayin mu na masu bin doka da oda kuma yan Nijeriya da suka san abinda suke yi kuma masu bayar da hadin kai, muna yin dukkan biyayyar data kamata ga hukuminin Nijeriya.”
A cewar sanarwar, “A shirye muke mu wanzar da shugabanci na gari da kuma bin doka da oda na gwamnatin Nijeriya.”
Kamfanin na MTN da yake gudanar da ayyukan sa a Nijeeiya, a ranar 16 ga watan Mayun shekarar 2019 ne ya zuba shiyar sa a kasuwar ta sayar da hannun jari ta NSE.
A bisa wannan ci gaban na kamfanin na MTN, dake gudanar da ayyukan sa a Nijeriya, dukkan masu ruwa da tsaki a kamfaninnna MTN, suna da damar suyi hada-hadar shiyar su a kasuwar ta sayar da hannun jari ta NSE.
Amma yan awowi bayan da masu zuba jarin da kuma masu ruwa da tsaki suka zuba, hakan ya basu damar yin hada-hada a kasuwar ta sayar da hannjn jari ta kasa.
Sun yi zargin kamfanin na MTN da ke gudanar ds ayyukan sa a Nijeriya, anyi cuwa-cuwa a cikin shiyar da ya yi hada-hadar ta a kasuwar ta sayar da hannun jari ta kasa don kara yawan tashin farashi a kasuwar ta sayar da hannun jari sama da sauran shiya da a ka yi hada-hada a kasuwar.
Bugu da kari, jaridar ta This day, ta ruwaito cewar, wadanda suka zuba jari a kasuwar ta sanayar da hannun jari ta kasa NSE da kuma masu ruwa da tsaki da suke jiran su sayi shiyar kamfanin MTN, zasu uya saye idan suna da bukata.
Hakan ya biyo bayan damar da mahukunta a kasuwar suma baiwa wasu harda kamfanin na MTN dake gudanar da ayyukan sa a Nijeriya a ranar Alhamis data gabata.
Amma duk da tunanin tabka cuwa-cuwar da ake zarhin kamfanin na NTN dake gudanar da ayyukan sa a Nijeriya ya yi akan shiyar sa, mahukunta a hukumar sadarwa ta kasa NCC ta nuna jin dadin ta akan shiyar da kamfanin na MTN ya zuba a kasuwar.
Mataimakin Shugaban Hukumar ta NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta a kwanan baya ya sanar da cewa, shiyar da kamfaninnna MTN ya zuba a kasuwar, yan Nijeriya zasu iya sayen shiya su kuma sayar, inda hakan zai tallafawa tattalin arzikin su.
Sai dai, zuba shiyar da kamfanin na MTN ya yi a kasuwar ta NSE, hakan ya nuna a zahiri akan kokarin da hukumar take yi na daukaka mahimmancin masu zuba jari na cikin gida a fannin sadarwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!