Connect with us

WASANNI

Meunier Zai Koma Arsenal Daga PSG

Published

on

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun tabbata da cewa kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Unai Emery, yana tattaunawa da dan wasan baya na kungiyar Paris Saint German, Thomas Meunier domin ya koma kungiyar.

Tun bayan da dan wasan ya bayyana cewa zai bar kungiyar PSG a wannan kakar aka fara alakanta shi da komawa manyan manyan kungiyoyi musamman a gasar firimiyar Ingila da suka hada da Manchester United da Arsenal.

Dan wasan dan kasar Belgium wanda ya buga wasanni 22 a kakar wasan data gabata a PSG ya bayyana cewa kungiyoyi da dama suna zawarcinsa domin yaje ya buga musu wasa kuma daya daga cikinsu an tabbatar da cewa Arsenal ce.

Kociyan kungiyar ta Arsenal dai ya san dan wasa Meunier sosai domin shine ya siyoshi a kungiuar PSG a shekara ta 2016 lokacin da yake koyar da kungiyar kuma a halin yanzu ance suna Magana domin sun sake haduwa a Arsenal.

Arsenal dai ta rabu da dan wasa Stephan Lichsteiner a karshen wannan kakar bayan ya koma kungiyar daga Jubentus a kakar data gabata kuma har yanzu dan wasa Hector Bellerin yana jiyya bai gama warkewa ba hakan yasa dole kungiyar ta sake fita neman dan wasan baya na bangaren dama.

Dan wasa Meunier wanda aka yiwa farashin fam miliyan 25 yana da ragowar kwantiragin shekara daya a PSG kuma tuni kungiyar ta bayyana cewa a shirye take data siyar da dan wasan ga duk kungiyar da take son siyansa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!