Connect with us

WASANNI

Ban Shirya Yin Ritaya Ba Yanzu, Cewar Ronaldo

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus dan asalin kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya ce ba shi da shirin yin ritaya ta gaggawa daga buga wa tawagar kwallon kafar Portugal wasanni.

A ranar Lahadin data gabata ne Portugal ta lashe sabon kofi da aka kirkira na Nations League, bayan da ta yi nasara a kan kasar Netherlands a birnin Porto da ci 1-0 wanda hakan yasa ta bkasance kasa ta farko data fara lashe kofin.

Ronaldo bai buga wa Portugal wasu wasannin cikin rukuni ba, amma ya taka rawar gani da ta kai kasar wasan karshe, wanda ya ci Switzerland kwallaye uku rigis a wasan daf da karshe ranar Larabar data gabata.

Dan kwallon na Juventus na fatan ci gaba da buga wa Portugal wasanni wadda take da matasan ‘yan kwallo karkashin Bernardo Silva na Manchester City wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasa a gasar.

Portugal ce ta lashe kofin nahiyar Turai a shekarar 2016, wadda take sa ran kare kambinta a shekara mai zuwa sai dai Ronaldo ya ce matsayar yana nan da koshin lafiya zai ci gaba da wakiltar kasarsa, domin abin da yake alfahari kenan.

Dan wasan, wanda ya kai shekara 16 yana yi wa tawagar kwallon kafa ta Portugal wasa, shi ne kadai ya rage daga ‘yan kwallon da Girka ta yi nasara a kansu a wasan karshe a gasar kofin nahiyar Turai a 2004
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!