Connect with us

RAHOTANNI

Majalisa Ta Tara: Wasu Bayanai Dangane Da Sabon Shugaban Majalisa Da Mataimakinsa

Published

on

Sanata Ahmad Ibrahim Lawan shi ne sabon shugaban majalisar dattawa ta kasa a Majalisa Tara, yayin da Sanata Obarisi Obie Omo-Agege ya zama mataimakinsa a shugabancin majalisar, wacce a ka kaddamar jiya Talata.

A jiya Talata, yayin da a ke kaddamar da majalisar ta tara ne Sanata Lawan ya zama shugaban majalisar, inda shi ma Sanata Omo-Agege ya zama mataimaki bayan da ya zarce tsohon mataimakin shugaban majalisar, Sanata Ike Ekweremadu, da yawan kuri’u.

Abinda ke biye wasu bayanai ne dangane da sabbin shugabannin kamar haka:

Sanata Ahmad Lawal:

An haifi Sanata Ahmad Lawan 12 ga watan Janairun shekarar 1959 (shekara 60 kenan).

-Ya zama sanata ne a shekara ta 2007.

-A fannin karatu, ya karanci fannin ilimin kasa da samaniya (Geography) a jami’ar Maiduguri, inda ya kara da ilimin na filaye sani da tsara (Land Surbey) a matakin digiri na gaba, sai kuma digiri na biyu da digirin-digirgir a fannin ‘Remote Sensing and Geographic Information System’ a jami’ar Cranfield da ke Birtaniya.

-Ya yi hidimar kasarsa a jihar Benuwai.

-Shi ne mafi dadewar sanata a cikin sanatocin jam’iyar APC.

-Sanata Lawan ya na wakiltar Yobe ta Arewa ne.

-Ya zama shugaban majalisar dattawa ta tara ne bayan da ya doke Sanata Mohammad Ali Ndume da kuri’a 79, yayin da Ndume ya samu kuri’a 28.

Sanata Obarisi Obie Omo-Agege:

-Shekarar sanata Omo-Agege 54 da haihuwa.

-Ya karanci fannin shari’a (lauya) a jami’ar Benin, inda ya yi hidimar kasarsa a shekarar 1987-1988.

-Ya yi digirinsa na biyu duk a fannin shari’a a jami’ar Tulane da ke New Orleans a shekarar 2002.

-Shi lauya ne da ya yi aikin lauyanci  a Najeriya da Amurka.

-Kafin zamansa sanata, ya rike mukamai daban-daban a jihar Delta, ya rika mukamin mai taimaka wa gwamnan jihar a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2005, inda daga baya ya yi kwamishinan ayukka na musamman a shekarar 2005 zuwa 2007. Ya kuma rike sakataren gwamnati a shekarar ta 2007.

-Ya ci kujerar sanata a cikin jam’iyyar LP, kafin daga baya ya yi wanka ya koma APC.

-Sanata Obarisi Obie Omo-Agege shi ne wanda ya shiga majalisa tare da wasu da a ke zargin ‘yan daba ne, inda suka tsere da sandar majalisa a ranar 18 ga Afrilun 2018, wani abu da ya zama kanun labarai da abin tattaunawa a lokacin.

-A sakamakon dauke sandar, an dakatar da shi na tsawon lokaci daga majalisar, inda daga bisani ‘yan sanda su ka cafke shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!