Connect with us

KIWON LAFIYA

Sarrafa Abinci Ta Muguwar Hanya Ya Sa Hukumar NAFDAC Kai Samame Abuja

Published

on

Hukumar kula da nagartar abinci da ingancin magungunguna ta kai hari wani wuri inda ake sarrafa zuma, ta hanyar da cikakkiyar tsafta a wurin cikin Abuja.

Farfesa Moji Adeyeye wadda ita ce shugaban Hukumar ta NAFDAC shine wanda ya bayyana hakan.

Shi wannan samamen da aka kai an samu labari ne ta hanyar kafafen sadarwa na zamani, wadda ta nuna ana yin wani abinci, wanda kuma wanda kuma majami’ar ”Upon the Rock Church of God”, wadda ke garin Durumi, Abuja ta hanyar da bata dace ba.

Jami’’an na Hukumar ”NAFDAC sun kai samamen ne wurin da ake sarrafa Zuma hanyar da bata dace ba.

”Mun kai shi wannan harin ne na samame akan labarin da muka samu ta hanyar labarin da aka dauka wanda aka dauka muka kalla ta bidiyo, wadda kuma an sayo ita Zumar ne daga wani kantin sayar da kayayyaki a Abuja. Wanda kuma ya sayi Zumar ne shine ya yada labarin inda ya nuna cewar Zumar da akwai matsala cikin ta.

”Shi dai ko kuma ita dai Zumar ana sarrafa ne a wata majami’a wadda ake kira da suna Rock Church of God, wadda kuma take cikin garin Durumi a Abuja, kamar dai yadda Adeyeye ya bayyana Durumi a Abuja kamar dai yadda Adeyeye ya bayyana’’.

Ta cigaba da bayanin cewar bayan da aka gwada ita Zumar an gano cewar bai dace mutum ya yi amfani da ita baa matsayin abinci, bayan kuma ita Hukumar ce ta yi ma shi kamfanin rajista.

”Binciken da aka yi ya nuna cewar shi kamfanin an yi ma shi rajista ne, cikin watan Disamba na shekarar 2018, an gano cewar dukkan wadansu ka’idojin da suka kamata an cika su.

”Amma kumadaga baya sai hannun agogo ya koma baya inda aka shiga yin zamba cikin aminci, saboda kuwa an shigar da wasu kayayyakin da aba kawo ko kuma sanar da ita Hukumar ba.

”Wasu daga cikin kayayyakin an gano cewar suna da jabun nambobin Hukumar akan su.

” Ann gwada wasu daga cikin sassan kayayyakin inda kuma aka gano kamare dai yadda rahoton ya nuna, abubuwan da aka fahimta dangane dasu, babu wata alamar gamsarwa hakika, idan kuma mutane suka ci gaba da mafani da su lafiyarsu na iya shiga cikin matsala, kamar yadda ta bayyana.”

Ta kara bayani inda ta ce Hukumar ta bayar da tabbacin zata kira duk su kayayyakin na abincin wadanda suka shiga kasuwa saboda sayarwa al’umnma, bayan nan kuma ta daukun matakin daya kamata akan wadanda suka aikata shi laifin na zamba da kuma shi kamfanin.

”Bugu da kari kuma an cigaba da daukar wadansu matakai wadanda kuma suke tsaurara ne, saboda a tabbatar da cewar shi kamfanin, ya bi sahun dukkan dokokin ita Hukumar, wannan kuma muddin idan shi kamfanin yana bukatar zai cigaba da yin harkokin shi.

”NAFDAC tana sanar da jama’a cewar tana ciga da daukar duk matakan da suka kamata, saboda kare lafiyar al’umma, wajen tabbatar da cewar kayayyakin sayarwa na abinci da kuma magunguna sun cimma dukkan sharuddan da suka kamata, musamman wadanda ita Hukumar ta ce sai an cika su tukuna.”

Daga karshe ta bayyana cewar wannan matakin an dauke shine saboda su kamfanonin su cigaba da tafiyar da harkokinsu, kamar dai yadda ka’idojin da aka shimfida suka nuna, wadanda kuma sun hada da wurin da aka ajiye su kayayyaki mai kyau da kuma, da kuma yadda ake rarrabasu wuraren da suka kamata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!