Connect with us

KASASHEN WAJE

Ta Rubuta Jarabawa Minti 30 Bayan Ta Haihu A Habasha

Published

on

Wata mata ta rubuta jarabawa a kan gadon asibiti minti 30 bayan da ta haihu a kasar Habasha.

Almaz Derese, mai kimanin shekara 21, ‘yar asalin garin Metu da ke yammacin kasar, ta shirya rubuta jarabawar ne kafin ta haihu, sai kuma aka dage jarabawar sakandaren saboda watan azumin Ramadan.

Ta fara nakuda ne a ranar Litinin wato kafin fara rubuta jarabawar farko.

Almaz ta ce rubuta jarabawa da ciki ba wata matsala ba ce, don ba za ta iya jira sai shekara mai zuwa kafin ta samu shaidar kammala karatunta ba.

Ta rubuta jarabawar Inglishi da ta harshen Amharic da kuma ta lissafi a asibitin ranar Litinin kuma za ta rubuta sauran jarabawar a cibiya jarabawar kwanaki biyu masu zuwa.

“Saboda ina zumudi in rubuta jarabawar, ban yi nakuda mai tsanani ba sam,” Mme Almazta ta shaida wa BBC.

Mai gidan ta, Tadese Tulu, ya ce sai da ya shawo kan makarantar kafin ta barta ta rubuta jarabawar a asibiti.

A kasar Habasha mata na yawan kaurace ma makarantun sakandare kafin su koma daga baya.

Mme Almaz tana son ta yi karatun shekara biyu nan gaba don ba ta dama share fagen shiga jami’a.

Ta ce ta gamsu da yadda ta rubuta jarabawarta , da kuma yadda ta ce yaronta na cikin koshin lafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!