Connect with us

MAKALAR YAU

Tarihi Mai Maimaita Kansa

Published

on

Abinda ke faruwa a Kano tsakanin Sarki da Gwamna tarihi ne ke maimaita kansa. Sai dai shi tarihi a wajen maimaita kansa, ba lallai ya faru daidai-wa-daida da yadda ya faru a baya ba, ya kan zo da nasa halayya daidai da mutanen da ya shafa da kuma zamanin.

A baya lokacin da Sadaunan Sokoto ke mulkin Arewa, sannan Sarki Sunusi na I ke sarautar Kano an sami rashin jituwa tsakaninsu yadda ta kai da dole a karshe sai da Sarkin ya yi murabus. Sarki Sunusi na I, kamar jikansa Sarki Sunusi na 2, a zamaninsa ya sami cikar duk wata ni’ima da Allah zai iya yiwa wani Dan Adam, domin ya fito daga Babban gida, ya na cikin sahun yan boko na farko masu basira ga ilimin addini, ga wadata ga kuma Sarauta mafi kwarjini a kasar Hausa.

Mutane da dama idan Allah ya yi musu ni’ima, su kan raina ni’imar ta hanyar rashin godiya, wato maimakon su tsaya matsayinsu sai su nemi wuce gona da iri. A lokacin Sardauna, ba wani mahaluki da ya sami shiga kuma Sardauna ke girmamawa tamkar Sarki Sunusi. Ta kai matsayin saboda aminci har surukutaka ce ta shiga tsakaninsu.

Sarki Sunusi na I ya gaji masauratar Kano a lokacin da mahaifinsa ya kai ta kokoluwar daraja, saboda ilimi ya fara habaka inda aka kafa makarantun boko, kasuwanci ya bunkasa saboda cinikin gyada wanda ya samar da gidajen attajirai irinsu Alhassan Dantata da su ka yi fice ba a Nigeria kadai ba har yammacin Afirka gaba daya.

Maimakon Sarki ya assasa abinda ya gada sai ya karkata akalarsa ga harkokin addini inda ya jawo Malamai irinsu Shehu Ibrahim Nyass. Ya kafa tarihi wajen kwasar jama’a duk shekara zuwa aikin aikin Haji tsawon shekaru goma da ya yi ya na mulki. A wannan zamani a na biyan Sarki albashin Fam 8000 amma wazirinsa fam dubu 1000 ya ke karba. Duk arzikin N.A. ta Kano na karkashin kulawar Sarki duk da dai akwai gwamna.

Rigimar Saradauna da Sarki Sunusi ta fara kunno kai tun a farkon shekarar 1961 a lokacin Sarki Sunusi na matsayin mukaddashin Gwamnan Arewa. Wata majiya ta nuna cewa Sarki Sunusi ya yi kunnen uwar shegu da dokar hana yin amfani da jiniya a Kaduna idan ban da Sardauna da Gwamna. Sannan a wasu lokatai ba ya isowa taro har sai Sardauna ya hallara. Mutane da dama sun fara zargin ya na wuce gona da iri a wannan mukami nasa.

Sannan a shekarar 1962 da aka fito da tsarin kwamishinonin gundumomi a arewacin Nigeria, Sunusi ya kalli wannan abu a matsayin kokarin rage karfin mulkinsa da Sardauna ke yi. Wani abin da ya kara assasa wannan rashin jituwa shine harkar addini da Sunusi ya maida hankali a kai tare da jawo sabuwar Tijjaniya kusa wadda ke karo da darikar Usmaniyya (wato masu bin koyarwar Dan Fodio) da Sardauna ya yi kokarin assasawa musamman a tsakanin yan boko da ma’aikatan gwamnati.

Sardauna, a kokarinsa na karkafa Usmaniya sai da ya kirkiri kyautar Usmaniyya (kwaikwayon kyautar Ingila ta OBE da MBE) wadda a ka fara baiwa Tafawa Balewa. Karkashin Usmaniyya a ka kafa kungiyar Jama’au Nasril Islam da kwamitin bada shawara kan al’amuran musulunci.

Sheikh Ibrahim Nyass ya fara zuwa Kano a shekarar 1951, a hanyarsa ta zuwa Makka, lokacin mulkin Sarki Abdullahi Bayero.

Alakar Sarki Alhaji da Ibrahim Nyass ta abokantaka ce ko ince Malami da Dalibi wadda su ke yi cikin sirri. Amma Sunusi ya maida alakar ta jama’a domin duk shekara, tsawon shekaru goma ya kan kwashi fadawa da Inyass da almajiransa su dunguma zuwa aikin Hajji, kuma an zargi ana amfani da kudaden N.A wajen wadannan harkokin na addini. Rigimar da ta kunno kai a wannan lokaci ita ce ta Kablu da Sadlu.

’Yan Tijjaniya, karkashin inyass na yin Kablu, kuma Nyass ya zo Kano ya yi Sallah da kablu a bainar jama’a. Rigimar kablu da sadlu ta kai har ga zubar jini, musamman a tarzomar Argungu a shekarar 1964. Kwamitin Malamai da Sardauna ya kafa, ya zauna an yi muhawara mai zafi kan wannan mas’ala yadda a karshe mafi rinjaye su ka kada kuri’a cewa a hana limamai yin kablu, abinda yan Tijjaniya a Kano ba su ji dadinsa ba.

A bangaren siyasa kuwa, Sunusi na I bai boye kansa ba wajen shiga dumu-dumu harkokin siyasa kasancewar shi ma ya taba  yadda hatta zabar wakilan majalisar yankin arewa (Northern House of Assembly) da na yan majalisar tarayya (Federal parliament) ya kasance mai wuka da nama a ciki. Sarkin ya kasance wani jogo a jam’iyya mai mulki, NPC, wadda ta rika amfani da sarakunan gargajiya wajen tursasawa yan adawa.

Da alaka ta tabarbare tsakanin Sardauna da Sunusi, gwamnatin Arewa ta kafa kwamitin Muffet a shekarar 1962 da zummar ya binciki lalitar N.A. ta Kano ya kuma mika rahotonsa ga Sule Gaya wanda ke matsayin Ministan kananan hukumomi. Sakamakon binciken ya sa an dakatar da kansiloli masu goyon bayan Sarki irinsu na lafiya da filaye Ado Sunusi (Dan Iyan Kano)  Babban Alkalin Kano Umaru, da Shehu Kazaure kansilan Ilimi da kuma Ahmadu Rufai Daura, wadanda a ka hana su fita daga gundumomin da ke su ke.

Sannan shi kansa Sarki ya gurfana a gaban Kwamitin Muffet domin kare kansa  ranar 13 ga watan Disamba inda Muffet din ya yi masa tambayoyi 25 a gaban Madakin Kanoda Sarkin Shanu. Kwamitin ya gayyaci hakimin Rano wanda a ke zargi da almubazzaranci da kudaden gwamnati kimanin fam 1868.

A karshe dai sakamakon wannan bincike ya haifar da murabus din Sarki da kan sa, sannan an yi garambawul a N.A. kuma a ka nada sabon sarki. Sakamakon wannan abu ya haifar da tarzoma a birnin Kano kuma magoya bayan Sunusi sun kafa jam’iyyar KPP (Kano people’s party) (wasu na kiranta jam’iyyar Sunusi) da zummar ganin cewa sun yi yaki wajen dawo da Sunusi kan kujerarsa.

Alamar da wannan kungiya ta dauka ita ce carbi, kuma sakamakon zagin Sardauna da su ka sa a gaba ya sa an kame duk manyan shugabanninta. Daga baya an sami rarrabuwar kawuna tsakanin shugabanninta duk da cewa ta sami goyon bayan talakawa musamman yan darikar Tijjaniya.

Idan mu ka dawo yanzu halin da ake ciki, Sarki Sunusi na II ya gaji duk irin ni’imomin da Allay yay i wa kakansa har ma ya zarta shi ta wasu bangarori, amma kash! Sai ya kasa amfani da kura-kuran tarihi da kakansa ya yi domin ya kauce musu, wato kamar tata-kamar-katanta inji bahaushe. Ya shigo mulki a mawuyacin hali cikin adawa ta gwamnatin tarayya amma maimakon ya na zuwa ya jawo mutane masu daraja da basira ya kafa dandali na hangen nesa wanda zai dawo da martabar Kano, sai ya ci gaba da halayyarsa ta babatu da soke-soke.

Ba na mantawa ranar da aka ba shi sandar mulki, wasu da mu ke kallon lamarin tare su ke cewa, to an kashe bakin tsada, ni kuma sai na yi wuf na ce to lallai ba ku san shi ba, har rantsuwa na yi ba zai daina tsoma baki cikin harkokin siyasa ba, abokaina su ka min ca, na yi shiru da cewar mu jira lokaci zai tantance tsakaninmu. Idan da Sarki Sunusi na II ya maida hankali wajen lalubo hanyoyi na warware matsalolin Kanawa tare da hada mutane waje guda, ba surutu da su ka ba, hakika da ya samarwa kansa wani bango da zai kare shi da al’ummarsa, yadda ko da ya yi suka babu yadda za’a yi ya fuskanci irin wulakancin da ya ke fuskanta.

Tashin farko ya fara rigima da Kwankwaso a game da hana tara Almajirai a gidansa ya na basu abinci, tare da fitowa fili ya na cewa ba wanda zai hana su ciyar da dukiyarsu yadda su ka ga dama. Allah ya takaita Kwankwaso ya zo karshen mulkinsa da labarin tuni ya canza.

Duk da cewa sukar da yayi wa Ganduje a cikin taro a Kaduna na maganar jirgin kasa ita ce dalilin da gwamnati ta janye maganar katafariyar kwangila ta dala Biliyan $1.5, kuma hakan ya ceci Kanawa daga wasoso da a ka so a yi da kudinsu. Amma Ganduje ya dauki abin a matsayin cin fuska wanda daga wannan lokaci aka saka damba na rigimarsu. A wancan lokaci Ganduje ya yi yunkurin tsige Sarki ba domin saka baki na manya a arewa ba.

Matsalar da ke tsakaninsu ta yi kamari a lokacin zabe inda Sarkin ya fito karara ya yi adawa da sake zaben Ganduje da ma na shugaban kasa. Wannan dalili ya sa, su na komawa kan kujera a ka lashi alwashin cin zarafinsa ta ko halin kaka. Wata majiya ta nuna cewa Aliko Dangote ya yi iyakar kokari wajen sake sassanta lamari amma sai gwamna Ganduje ya bada zabi uku, wato ko Sarkin ya yi murabus ko a tsige shi ko kuma ya kirkiri sabbin masauratu.

Kin yin murabus da tsige shi ya kare da daddatsa masauratar Kano zuwa gida hudu. Wannan abinda Ganduje ya yi akwai rashin adalci ga Kanawa da kuma rashin nuna damuwa ga maslahar jama’a. Domin matsala ce tsakanin Gwamna da Sarki, ban ga wata hujja da za’a jefa Kanawa cikin rikicin ba, wanda ya kawo rarrabuwar kawuna cikin al’umma.

Tunda shi Ganduje ya lashi takobin fansa, to kamata ya yi fansarsa ta tsaya kan sarkin kawai, wato ya kira shi ko ya sanar da shi cewa ya ba shi wani kayyadadden lokaci, ko dai ya kawo takardar murabus ko ya sa a tsige shi. Haka Sardauna ya yi wa kakansa, domin kaucewa jefa al’umma gaba daya cikin rikicin na su. Amma shi wannan gogan naka saboda masalahar al’umma ba ta gabansa ya gwammace raba masauratun.

A wannan hali da ake ciki na matsin tattalin arziki, sabbin masauratun za su rika lakume kudade da bai kamata su je gare su ba, kuma an kara wa gwamnati nauyi babu gaira babu dalili. Wani aboki na daga masaurata Gaya, ya yi min bayanin irin illar da kirkirar sabbin masauratun ta kawo musu domin an tarwatsa hakimansu zuwa Bichi, Karaye da Rano. A cikin fushi da rashin lissafi na Ganduje, maimakon ya tsaya tsayin daka cewa sai ya cire Sarkin shi kadai, sai ya gwammace da kirkirar sabbin masaurautun.

Shi kuma Sarki, ya gaza gadar kakansa wajen kare ragowar kimarsa ta yin murabus, ya gwammace a yi ta turka-turka kowacce iri ce matukar ya na kan kujerarsa. Don haka son kai irin na wadannan shugabanni guda biyu ya gwammace damalmala mu’amalar al’umma a kan son ran su. Dukkansu babu wand aba maslaharsa it ace gaba da ta al’umma ba.

Sannan wani katon abin kunya shine idan ka cire Aliko Dangote, ba wani wanda ya jajirce ganin cewa an samo bakin zaren. Musamman shugaban kasa wanda ya ja bakinsa yay i shiru, abinda ba daidai ba ne domin dai ko ba daga yankin ya fito ba, idan ya na kishin Kanawa, ya kamata a ce ya tsawatar. Menene amfani shugaban da a kullum ana fitina sai dai ya zama dan Kallo?

Shin ya na zato Allah ba zai tambaye shi ba? Ko da yak e wani aboki ya bani labarin cewa a hanyarsu daga Abuja zuwa Adamawa wajen rantsar da gwamna su tare da wani Babban Sarki a Arewa a cikin jirgi inda ya tambaye shi cewa me yasa manyan arewa su ka ki shiga rigimar Sarki da Ganduje, musamman su Sarakuna?

Ya bashi amsar cewa “Mu sarakunan arewa mun yi gwamnan Babban bankin Nigeria ne? Ko mu gogaggun yan boko ne? Sarkin ku ya raina kowa, bay a ganin kowa da gashi, hatta shugaban kasar (Buhari) duk inda ya zauna zaginsa yak e yi kuma ana komawa a fadawa shugaban kasa.” Wannan alama ce cewa shugabannin arewa na da hannu cikin wannan rikici, kuma Bahaushe na cewa “Idan gemun dan uwanka ya kama da wuta ka shafa wa naka ruwa” Karin maganar da wani ya canza ta da cewar “Ka nemo ruwa a kashe wutar gemun nasa” Tunani irin wanda ya gagare mu a arewa, kuma idan ba mu gyara ba, wallahi “Abinda ya ci Doma ba zai bar Awai ba.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!