Connect with us

TARIHI

Tarihin Kasar Bauchi

Published

on

Cigaba daga makon jiya.

Kashi Na Biyar

A lokacin da rundunoni biyu suka fuskanci juna, watau rundunar Sarkin Bauchi Yakubu da ta Mayaki Kalumba, sai kowannen su ya buga tambarinsa, mayaKa suka fadawa juna da sara da suka, Kura ta turnuKe sama, sama ta cika da hayaki, yaki yayi zafi, ya huru, rana ta zama misalin dare, ba a jin kome sai Karar Karfe da tsarkiyar baka.

Sannu a hankali sai duhu ya Kara duhu, har ya zama abokin gaba baya ganin wanin sa. Sai Sarkin Bauchi yakubu ya baiwa jama’ar sa umarnin suyi ta harbin duhun har sai da duhun ya yaye aka ga Kalumba ya gudu, taron sa kuma ya watse, ya bar tambarinsa da tutarsa da laimar sa da tarkacensa da dukkan wani abu da yake mai nauyi anan suka bar shi suka gudu.

Daga nan sai Yakubu ya tatttara kayayyakin na su ya aike da su wurin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, sannan ya koma gida Bauchi cikin farin ciki saboda taimakon da Allah Ta’ala yayi gare shi.

Bayan wannan sai Yakubu ya sake tashin yaki zuwa Misau, ya yake su, ya zauna a Kofar garin su kwana talatin, ya hana su fita har sai da yunwa ta tsananta garesu ya zama suna cin dawakai da jakuna da sauran ababen dake hannunsu.

Da abin yayi tsanani sai suka watse, Yakubu ya kama na kamawa saura kuma suka dai-daice a duniya, suka bar birnin su wofi babu kowa.

Yakubu ya koma gida dauke da ganima mai yawa, ya zauna tsawon wasu shekaru a gida, sannan ya tashi da yaki zuwa Tsaure, shikuwa gari ne a arewacin Bauchi, ya iske su suna sauraron sa, alhali bai san sunyi dakon zuwan sa ba, har sai da ya zo kan kan kan da su, sannan suka fada masa da yaki, ya yake su da yaki mai tsanani har sai da ya kore su, ya kashe na kashewa, saura suka gudu suka bar gidajensu, shi kuwa ya Kone gidajen sannan ya koma Bauchi tare da jama’ar sa.

Bayan wannan sai ya Kara yin shirin yaki zuwa Tufi, nan ma ya same su sun taru a bakin babban dutsen su, ya hau su da yaki. Amma sai da yayi yaki dasu tsawon shekaru biyar sannan yaci galaba akansu.

Wannan kuwa shine Karshen yake yaken Sarkin Bauchi na farko Yakubu, domin daga shi bai sake fita yaki ba Allah yayi masa rasuwa. Dafatan Allah ya jiKansa amin

Kashi Na Shidda

Bayan rasuwar Sarkin Bauchi Yakubu sai dansa Ibrahimu ya gaje shi. Shikuwa sai da ya shafe shekaru arba’in bisa karagar mulkin Bauchi.

A shekatar farko ta mulkin Ibrahimu ne ya tara runduna tare da tafiya Angas yaki. A can ne ya buga gagarumin yaki da mutanen, ya kashe na kashewa ya kama na kamawa, sannan ya koma Bauchi da ganima mai yawa.

Babu jimawa sai ya sake fita yaki zuwa Montwal, yaje ya kore su sannan ya koma Bauchi da zama..

A shekarar mulkin sa ta biyu ya tafi yaki da wani mayaki mai suna Hamza. Ya gamu dashi ya yake shi, ya watsa taron rundunar sa, ya kashe na kashewa ya kama na kamawa, sannan ya koma gida Bauchi.

Bayan shekaru biyu kuma sai ya ciri runduna zuwa Tabula, ya zauna a Kofar ta tsawon shekaru takwas. A cikin shekara ta bakwai da zaman sa a Kofar Tabula ne dan uwan sa Salmanu ya mutu yana tare dashi. Jim kadan da faruwar haka sai ya Kulla amana da kafiran wajen mazauna dutse sannan ya koma gida.

Sai dai, Ibrahim sarkin Bauchi ya koma gida da shekara daya ne ya samu labarin cewa dukkan kafiran duwatsu sun warware amanar da aka Kulla dasu.

Don haka ya shirya ya ƴi ya tafi Das da ake kira Bununu (sunan Sarkin su Mummini) ya yake ta. Daga nan ya tafi Duwa tare da sarkin Kano da Sarkin Zaria da Sarkin Gombe da Shehun Borno suka yake ta.  Daga nan sai ya tafi Gamawa tare da Sarkin Kano suka yake ta.

Bayan wannan kuma sai ya tafi Duguri yayi yaki da mutanen ta, sannan ya sake komawa Das yayi yaki, ya kara komawa Duguri ya sake gwabba yaki.

Haka kuma Sarkin Bauchi Ibrahim ya yaki Jimbim, amma daga nan bai sake fita yaki ba, sai ya tafi Rauta ya zauna yana aikawa da hare hare zuwa abokan gaba, har kuma ya nemi a tuɓe shi daga sarauta a dora dansa Usmanu.

Abinda ya nema kuwa shi ya samu, inda aka nada dansa Usmanu sarki, ya koma Bauchi da zama, yayin da mahaifin sa Ibrahimu ya cigaba da zama a Rauta.

Shekaru sama da dubu daya akwai mutane a yankunan Bauchi, amma babu takamimen Kabilun su ko harsunan su. Sai dai ana tsammanin kasancewar su jikokin Kabilun NOK da a ka ce sun rayu wani yanki na Arewacin Nigeria. Sannan tana iya yiwuwa alaKa ta shiga tsakanin su da Kabilun Kwararrafawa da jikokin su jukunawa wadanda suka kafa daulolin su a kusa da wannan yanki na Bauchi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!