Connect with us

RA'AYINMU

Hadarin Yi Wa Sarakunanmu Lahani

Published

on

Ko shakka babu, Sarakuna a Nijeriya sun jima suna baiwa al’ummarsu gudunmawa ta fuskoki daban-daban, har kuwa bayan zuwan Turawan mulkin Mallaka da tsarin mulkin demokradiyya. Wadannan Sarakuna, sun jima suna Shugabantar al’umma suna kuma ci gaba da kula tare da tafiyar da al’adunmu wanda a koda yaushe kan taimaka mana wajen sanin asalinmu da kuma inda muka fito.

Babban amfanin Sarakunan Gargajiya a wancan lokaci shi ne, tafiyar da harkar shari’a da mulki da kuma abin da ya shafi harkokin addini. Suna kuma tafiyar da harkokin al’umma yadda ya kamata, don kuwa al’ummar sun yarda cewa, su ne Shugabanninsu na bangaren addini da sauran al’amuran rayuwa. Shi yasa suke bin su sau-da-kafa ko kara suka gindaya ba sa iya tsallakawa.

Duk da cewa a wancan lokacin, ana tilastawa talakawa da masu karamin karfi su biya haraji, wannan ai da ma ba wani sabon abu ba ne. dalili kuwa, da dan abin da suke samu ne suke iya tafiya da harkokin mulkin da sauran al’amaran da suka shafi al’ummar da suke mulka.

Haka zalika, a kan wannan tsari ne aka ci gaba da dorawa har bayan zuwan Turawan mulkin mallaka a wannan kasa, inda Sarakuna suka rika karbar umarni daga wurinsu, suna sakko da shi zuwa wajen talakawan da ke karkashinsu. Tun a wannan lokaci, haka tsarin ya ci gaba da kasancewa Sarakuna na wakiltar al’umma tare da tafiyar da harkokinsu duk da cewa, tsarin ba na demokradiyya ba ne musamman a yankunan Arewacin Nijeriya da kuma na Yarbawa.

Har ila yau, kamar yadda Turawan mulkin mallakan suka tarar da tsarin Masarautunmu, haka suka tafi suka bar shi a yadda yake ba tare da sun canja masa wani tsari ba. Kazalika Sarakunan gargajiyar nan, su ne suka tsaya tsayin daka wajen fafutukar samun ‘yancin kai da ya yi sanadiyar tabbatar da mulkin demokradiyya da yanzu ya ba mu ‘yanci ko damar da za mu iya mulkin kanmu da kanmu. Sannan wasu daga cikin su saboda irin tasirin da suke da shi da kuma dalilan siyasa ya sa ake sanya su cikin harkokin da suka shafi demokradiyya (Sarakuna).

Duk da cewa, akwai wata rawa da ake ba su damar takawa a cikin tsarin na demokradiyya, amma duk da haka ‘Yan siyasa a koda yaushe cikin zargin Sarakunan suke. Koda yake, dukkanin irin wadannan abubuwa ko kadan ba su taba faruwa kafin ko bayan zuwan Turawan mulkin mallakan ba, idan aka kwatanta da abubuwan da ke faruwa a halin yanzu.

Idan aka yi la’akari da irin farmakin da ake kaiwa Sarakunan a halin yanzu, ana iya cewa ko shakka babu ba karamin hadari suke kan fuskanta ba. Wannan dalili ne ya sanya wannan gidan Jarida yake bayyana damuwarsa musamman kan ire-iren hare-haren da ake kai musu babu kakkautawa. Don kuwa, kamar yadda wasu rahotanni ke bayyanawa daga kafafen yada labarai na wajen kasar nan, cewa suke yi wasu daga cikin Sarakunan wannan kasa na fuskantar wani mummunan yanayi.       

A mahangar wannan Kamfanin Jarida, Sarakunan gargajiya wadanda a koda yaushe ke tare da al’umma, ya kyautu a daina sanya su cikin zarge-zargen wadanda ake zargi na da hannu a cikin harkokin da suka shafi ta’addanci da sauran matsalolin da ake fama da su na tabarbarewar tsaro. Kamar yadda muka taba kalubalantar hakan a wannan shafi cewa, ko kadan bai dace a rika alakanta su da irin wadannan abubuwa da ke faruwa ba.

Don haka, wajibi ne mu rika yin taka-tsantsan don gudun kada mu raunana kima tare da darajar da suke da ita a wajen al’ummar da suke jagoranta. Dalili kuwa mu a namu ganin, rawar da Sarakunan gargajiya ke takawa a tsakanin al’umma ya fi karfin na siyasa kadai. Don kuwa, su ‘Yan siyasa zuwa suke yi su tafi, amma su a koda yaushe suna nan tare da al’ummarsu.

Shi yasa muke ta kokarin nusasshe da ‘Yan siyasa kan su fahimci hadarin dora al’umma a kan tunanin Sarakunansu na gargajiya da ke Shugabantarsu wasu mutane ne da ake hada baki da  su ake cutar da su ko kuma ake karkashe su tare da hadin bakinsu, don haka su yi watsi da su. Babu shakka yin hakan ba zai haifar mana da Da mai ido ba.

A karshe, kiran da muke sake yi ga Shugabannin siyasa shi ne, wajibinsu ne su hada kai da Sarakunan gargajiya, don kuwa dukkanin su kowanne na da nasa amfanin wajen tafiyar da harkokin al’umma da kuma ci gabansu.aboda haka, wajibi ne a ci gaba da baiwa Sarakunan gargajiya mutuncinsu da kuma darajar da Allah Ya ba su.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: