Connect with us

KASUWANCI

Abinda Ya Janyo Jirgin Sama Na Kamfanin Air Peace Ya Samu Hadari

Published

on

Jirgin sama na Kamfanin Air Peace ya rikirkito tare da fasinjijin dake yake dauke dasu a a garin Fatakwal.

Lamarin ya auku ne a ranar Asabar a loacin da jirgin saman ya taso daga Abuja zuwa Fatakwal.

An ruwaioto cewa, lamarin ya aku ne sakamakon rowan sama mai karfin gaske.

Har ila yau, ance matukin jirgin ya yi iya kokarin san a daidai alamura, amma sai da jirgin ya yi sabi zarce ya tunkari daji dauke da fasinjojin da kuma ma’aikatan dake cikin jirgin.

Iftila’in ya auku ne da misalign karfe 3:42 na yammacin ranar ta Asabar kuma babu wanda ya rasa ransa ko jin wani ciwo.

Babbar Manajan Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Kasa Uwargida Henrietta Yakubu a cikin sanarwar data fitar ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce, babu ran day a salwanta ko wani jin ciwo.

Uwargida Henrietta Yakubu ta kara da cewa, jirgin ya kauce hanya ya auka cikin daji kuma direban jirgin saman na Air Peace ya yi namijin kokari wajen tsyar da jirgin.

Ta danganta aukuwar lamarin a kan tsananin rowan sama da aka yi a ranbar ta Asabar.

Shi kuwa wani Babban jami’ain gudanar da ayyuka na kamfanin jirgin saman Oliwatoyin Olajide, ya sanar da cewa, rowan sama ne ya janyo aukuwar lamarin sakamakon ambaliyar ruwa a titin saukar jirgin.

Oliwatoyin Olajide ya kuma jinjinawa namijin kokarin da direban jirgiun ya yi wajen shawo kan jirgin don ya sauka a cikin sauki.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: