Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Dalilin Da Ya Sa Na Kashe Mahaifiyar Budurwata – Wani Tsohon Dan Sanda

Published

on

Wani tsohon dan sanda wanda a ka sallama daga aiki mai suna, Christian Ogwu, wanda ya harbe mahaifiyar budurwarsa har lahira, mai suna Beronica Obiejiogo, ya bayyana dalinlin da ya sa ya aikata lamarin. Ogwu ya bayyana cewa, ya aikata wannan lamari ne, saboda mahaifiyar ta shawarci diyar nata mai su na Blessing Obiejiogo, a kan kar ta aure shi. Wanda a ke zargin ya harbe matar har lahira a gaban idanun yaranta a kusa da gidansu da ke yankin Otolokpo cikin karamar hukumar Ika ta arewa ta Jihar Delta.

Iyalan marigayiyar sun kai kara wurin Sufetan ‘yan sanda na kasa, Adamu Mohammed, inda ya umurci tawagar ‘yan sanda wanda mataimakin kwamishina, Abba Kyari ya ke jagoranta, da su cafke wanda a ke zargin. An samu nasarar cafke wanda a ke zargi ne a wani banki da ke cikin garin Fatakwal bayan wata biyar da aikata lamarin.

A cikin bayaninsa, wanda a ke zargin ya bayyana cewa, “ni tsohon dalibin jami’ar Benin ne. Na shiga aikin dan sanda a shekarar 2000, amma an kore ni daga aiki baya da ’yan fashi da makami su ka sace min bindiga a wani shinge na ‘yan sanda lokacin da na ke cikin maye. “Lambar inifon dina shi ne, 371416, na samu horo daga kwalejin ‘yan sanda da ke Ikeja cikin Jihar Legas, amma an tura ni aiki a ofishin ‘yan sanda da ke garin Iho cikin Jihar Edo, inda a nan ne na yi aiki na tsawon shekaru biyar kafin a kore ni daga aiki, sakamakon sace min bindiga a wani shingen ‘yan sanda.

“Sakamakon gudanar da haramtacciyar kasuwanci da na ke yi, na hadu da budurwa mai suna Blessing Obijeogoh, a kwalejin kimiyya da ke cikin Jihar Delta, inda a nan ne ta ke karatu. Ta bayyana min cewa ba ta da miji, mun fara soyayya inda ta kai har sai da na yi mata ciki, an zubar da cikin. “Ta bayyana min cewa, bai kamata ta haiho da ni ba, saboda ban san iyayenta ba. A cikin watan Afrilun shekarar 2018, ta kai ni wurin iyayenta, inda su ka bukaci in dawo domin gudanar da tasre-tsaren aure.      

“A ranar 7 ga watan Satumbar shekarar 2018, na kara komawa wajen iyayenta, inda su ka yi min lissafin kudin aure. A cikin watan Oktoba, ta bayyana min cewa ta na da juna biyu, na ce mata babu matsala, sai mu hanzanta mu yi aure. Mun ijiye cewa, za mu yi aure a ranar 27 ga watan Disamba, na ba ta kudi masu yawa domin ta sayi kayan aure. “A ranar 5 ga watan Disiamba, ta kira ni a waya salula cewa, ita ta na kan hanyar zuwa Asaba, inda za mu zauna bayan mun yi aure, na ta kokarin kiran ta a wayarta amma ba ta dauka ba.

“Wani dan uwanta mai suna Friday ya bayyana min cewa, Blessin ba ta da lafiya, kuma su na asibitin Asaba tare da mahaifiyarta za a zubar mata da ciki. Na je asibitin domin in ga likitan, amma ban samu ganin Blessing da mahaifiyarta ba. “Nan ta ke na gane cewa akwai wani abu, na kira ta domin in ji yadda ta ke ji, sai ta bayyana min cewa ta na gidan kawarta a cikin garin Asaba. Na je gidan, amma ban samu ganin ta ba, na jira har na tsawan wuni daya, inda daga nan na daina neman ta. “Abun mamaki, a ranar 21 ga watan Disambar shekarar 2018, sai ta kara kira na, inda ta bayyana min cewa ta na kan hanyar zuwa Legas, na fusata kwarai a wannan lokaci ganin yadda Blessing tare da mahaifiyarta su maida ni wawa. Sai na je wajen wani abokina mai suna Steben.   

“Na fada masa dalilin da ya sa na je wurinsa, Steben ya shawarce ni a kan in kwantar da hankalina, amma na fusata inda na ke so na dauki kwararan mataki a kan yarinyar da kuma mahaifiyarta. Na bukaci Steben ya ba ni aron bindiga tare da harsashi guda biyu, inda na ba shi kudi naira 10,000.  “A ranar 26 ga watan Disambar shekarar 2018, na tafi kauyen su Blessin tare da wannan bindiga. Na yi bincike sosai inda na gane ta na cikin garin, amma lokacin da na kira ta a waya, sai ta bayyana min cewa ta na Legas. Na tafi wani shago kusa da gidasu, inda na sayi kwalban giya tare da kwayar fakitin Tiramadol. Na sha su a tare, domin yin rashin mutunci.

“Lokacin da na tsima, sai na ga mahaifiyar tare da karamin kaninta su na zuwa inda na ke, na isa kusa da su inda na ciro bindigar na harbe mahaifiyar Blessing, ban bar wurin ba har sai da na ga mutuwar takafin na bar wurin.”

Za a gurfanar da wanda a ke zargin a gaban kotu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: