Connect with us

MANYAN LABARAI

Gwamna Inuwa Ya Nada Sarkin Gwambe A Matsayin Amirul Hajj Na Jiha

Published

on

Gwamnan jihar Gwambe Muhammad Inuwa Yahaya ya nada sarkin Gwambe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar na III a matsayin Amirul Hajj na aikin hajjin da za’a gudanar na wannan shekarar.

A cewar wata sanarwa da babban mataimakin shi na musamman kan watsa labarai da kafofin sadarwa, Ismaila Uba Misilli ya sanar da cewa kwamitin zai yi aiki da hukumar jindadin alhazai ta jihar da sauran hukumomi don tabbatar da an gudanar da aikin hajjin wannan shekarar cikin walwala da kwanciyar hankali.

Kwamitin mutum 11 ya hada da Barr. Zubair Muhammad Umar a matsayin mataimaki da Bala na Waja Chiefdom da Danjuma Mohammed da Malam Ado Gabanni da Sheikh Adamu Dokoro da Sheikh Adamu Girbo da kuma Sheikh Usman Isah Taliyawa a matsayin ‘ya’ya kwamitin.

Sauran su hada da Sheikh Naziru Idrisa Umar da Hajiya Farida Sulaiman da Hajiya Uwani Shuaibu Gara da kuma Saidu Shehu Awak a matsayin sakataren kwamitin

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Alhamis din makon da ya gabata gwamna Yahaya ya nada Sa’adu Hassan a matsayin babban sakataren hukumar jin dadin alhazan jihar
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: