Connect with us

WASANNI

Kociyan Najeriya Ya Yi Kuskure

Published

on

Tsohon kaftin din Super Eagles ta Najeriya, Joseph Yobo, ya bayyana cewa kociyan Najeriya, GernoT Rohr yayi kuskure da bai fara buga wasan da Najeriya ta samu nasara daci 1-0 ba tare da Ahmad Musa ba da Idion Ighalo.

Yobo ya bayyana hakane yayin wata tattaunawa da manema labarai a jiya bayan an tashi daga wasan da Najeriya ta samu nasara akan kasar Burundi daci 1-0 ta hannun dan wasa Idion Ighalo wanda ya shigo wasan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Tsohon dan wasan ya cigaba da cewa sai da Ahmad Musa da Ighalo suka shigo wasan sannan aka fara samun damarmaki saboda haka dole a wasan da Najeriya zata buga na gaba da kasar Guinea sai kociyan yayi amfani da ‘yan wasan biyu.

“Sai bayan da suka shigo sannan suka canja wasan saboda sun nuna kwarewa da kuma sanin makamar aiki sakamakon sun buga wasanni daban daban ciki har da kofin duniya saboda haka kwarewarsu ce tasa aka samu nasarar” in ji Tsohon dan wasan na Eberton

Ya cigaba da cewa “Akwai matasan ‘yan wasa a cikin tawagar kuma nan gaba sune zasu zama jagororin tawagar ta Najeriya nan gaba sai dai akwai bukatar manyan ‘yan wasa su dinga kasancewa da su a cikin fili domin taimaka mu su.”

Nigeriya ce dai yanzu a mataki na farko acikin rukuni na B bayan samun nasara a wasan farko sai kuma Madagascar a mataki na biyu bayan sun buga canjaras 2-2 da kasar Guinea sai dai Najeriya za ta buga wasanta na gaba da kasar Guinea a ranar Laraba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: