Connect with us

LABARAI

Safiyya Foundation Ta Gudanar Da Taron Ranar Masu Cutar Sikila A Zariya

Published

on

A ranar Larabar da ta gabata, wacce ya yi da daidai da 19 ga Yuni da hukumar lafiya ta majalisar dunkin duniya ta ware, domin yin waiwaye, adon tafiya ga halin da ma su dauke da cutar Amosanin jini ke ciki a sassan duniya, wata gidauniya mai suna ‘Safiyya Sickle Cell Foundation’ ta jigoranci taro tare dam asana kiwon lafiya da kuma su dauke da wannan cuta a Zariya.

Farfesa Abdul’aziz Hassan shi ne shugaban tsangayar kula da jini na asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, shi ne kuma babban bako mai jawabi a wajen wannan taro day a gudana a katafaren dakin taro na kwalejin Barewa da ke Zariya, tun farko ya jawo hankalin ma su dauke da wannan cuta ta Amosanin jinni da su rika bin dokokin da likita ya dora su a kai.

Ya ci gaba da cewar, duk wanda ke dauke da wannan cuta, wajibi ne da ya rika zuwa asibiti a lokacin da likita ya ce ya je, tare da shan magungunan da likita ya yadda ya rika sha a duk rana, ba tare da sakaci ko kuma daukar wani ko kuma wasu matakan juya wa magani baya ba.

Da kuma Farfesa Abdul’aziz ya juya ga wannan gidauniya da ta shirya wannan taro, sai ya yaba ma su, musamman na yadda wannan gidauniya ke tallafa wa ma su dauke da wannan cuta, da kuma yadda ta ke rubuta bayanai a takardu, domin kara ilmantar da ma su dauke da wannan cuta, matakan da suka dace su rika bi, matukar wannan cuta na tare da su.

A na ta jawabin, fitacciyar likitan da ke asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Farofesa Aisha Indo Mamman ta yi dogon bayanai kan matakan da mai dauke da wannan cuta ya dace ya dauka ko kuma ta dauka, tun daga zuwa ga likita da kuma shan magani a kan lokaci, kamar yadda likita ya bayar da umurni.

Shi ko Shekh Malam Bashir Magaji (Basharata), malamin addinin Musulunci kuma masanin kiwon lafiya, shi a jawabinsa, jawo hankalin iyaye ya yin a lallai ne mayar da hanlkali, wajen yin gwajin jinni a duk lokacin da batun aure ya taso, a tsakanin wadda ake so da kuma wanda ya ke son yin auren.

A cewar Shekh Bashir Basharata, matukar aka dauki matakin yin gwajin jini kafin yin aure, babu shakka, kamar yadda ya ce an dauki matakin farko na dakile yaduwar wannan cuta ta Amosanin jinni da ke durkusar da al’umma ta yadda suke rayuwa.

Sai dai kuma fitaccen Malamin addinin musuluncin ya nunar da cewar, bincike ya tabbatar, duk wanda ke dauke da cutar Amosanin jinni, za ka same shi, ko kuma za ka same su da hazaka, musamman in an tashi batun haddar Alkur’ani mai girma.

A zantawa ta da wakilinmu jim kadan bayan kammala taron, Hajiya Maryam Ado, daya daga cikinwukar yankar Magana ce a wannan gidauniya ta Safiyya Foundation,ta ce, Safiyya wadda ta fara tunanin kafa wannan gidauniya, kuma ta yi tunanin kafa wannan gidauniyar ce, a dalilin wahalar da ta ke sha kasancewar ta mai wannan cuta ta Amosanin jini.

Hajiya Maryam ta nunar da cewar, ana saura kimanin wata uku Safiyya ta bude wannan gidauniya, sai ta rasu, ‘’amma sai mu ‘yan uwanta na jini, mu ka cika ma ta wannan buri na tan a ganin ta kafa gidauniyar da za ta rika tallafa wa ma su cutar Amosanin jinni, wanda zuwa yau, a karkashin wannan kungiya, a kwai ma su dauke da wannan cuta fiye da dari biyu da mu ke tallafa ma su da maganin dare da kuma rana.’’

Wannan taro, ya sami halartar dalibai da kuma masana kiwon lafiya da su ka fito daga sassan ciki da kuma wajen Zariya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: