Connect with us

LABARAI

Jiragen Ruwa 11 Sun Iso Tashar Ta Legas Shake Da Fetur

Published

on

Jiragen ruwa 11 ne suka iso tashar Jiragen ruwa ta Legashake da man fetur da kuma sauran kayayyakin amfanin yau da kullum. Jiragen wadanda a yanzun haka suke jiran da a sauke kayan da suka dauko a tashoshin Apapa da Tin Can a Legas, kamar yanda hukumar kula da tashoshin Jiragen ruwan ta ambata a cikin mujallarta wacce take wallafawa a kullum-kullum, a kan yanayin da tashar ke ciki a can Legas.

“Biyar daga cikin Jiragen 11 suna jira ne a sauke man fetur din da suka dauko, a sa’ilin da sauran shidan kuma suke dauke da kwantenoni  da kuma takin zamani, in ji hukumar ta NPA.

Hukumar kuma ta ce, ana sa ran isowar wasu Jiragen guda 29 a tashar Jiragen ta Legas a tsakanin 25 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli.

Hukumar ta ce, Jiragen 29 za su shigo ne dauke da kayayyaki daban-daban da suka hada da Gishiri, kananan taragogin mota, Suga, takin zamani, malta, alkama, fetur da kwantenoni.

Ta kuma kara da cewa, Jirage 17 za su sauke alkama, mai, kayayyaki daban-daban, karafa, kwantenoni, man dizel, fetur, man Jiragen sama, suga da kuma kwantenonin da babu komai a cikinsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: