Connect with us

TATTAUNAWA

Kokarin Gwamnati Na Bunkasa Noma: Rijiya Ta Bayar Da Ruwa Guga Ya Hana

Published

on

YUSUF MUHAMMAD INUWA GWARZO shi ne shugaban kungiyar masu noma waken soya ta jihar Kano, a tattaunawarsa da SABO AHMAD KAFIN-MAIYAKI a ofishinsa da kan titin zuwa gidan zu a cikin garin Kano, ya bayyana yadda shirin gwamnatin tarayya na bunkasa noma ke cin karo da matsaloli. Matsalolin da suka hada da rashin samun cikakken amfanin shirye-shiryen gwamnati na bunkasa noma ga manoma, da tsaurara hanyoyin samun rancen gwamnati, a karshe ma har da wahalar da manoman ba tare da sun samu rancen ba.  Ga kuma yadda tattaunawar ta kasance:-

Gabatarwa

Sunana Yusuf Muhammad Inuwa Gwarzo, shugaban kungiyar masu noman waken soya na jihar Kano.

Kowace gwamnati na zuwa da irin nata tsare-tsaren na bunkasa noma, domin wadata kasa da abinci da samar da ayyukan yi, ya ya za ka kwatanta tsare-tsaren wannan gwamnati da na sauran gwamnatocin da suka gabata.

Gwamnatin da ta gabata ta zo da tsare-tsaren bunkasa noma yadda za a bunkasa noman kowane amfani har zuwa sarrafa shi. A tsarin gwamnatin da ya gabata an dinga aikowa da manoma taki ta hanyar alat a waya, inda manomi zai je ya biya kudi sannan ya je dauka.

Bayan zuwan wannan gwamnati sai ta zo da irin nata tsarin a kokarinta na yaki da cin hanci da rashawa a bangaren noma, saboda haka sai ta ga a irin wancan tsarin ana karkatar da wasu kayan da aka ba manoma.

Saboda haka wannan gwamnati ta ce, an soke tallafin da ake bayarwa na wajen iri da magani, an canza wannan tsari zuwa, dukkan wani shirin bunkasa noma ya koma karkashin Babban Bankin Nijeriya. Akwa  hukumomi da bankunan kasuwanci karkashin Babban Bankin wadanda ta hanyarsu ne za aiwatar da wadannan shirye-shirye.

Sannan akwai hukumar NIRSAL wadda ita ma an kirkireta ne domin taimakawa manoma wajen rage radadi kan asarar da za su iya yi a lokacin noma. Saboda haka aka ba wannan Hukuma umarnin cewa, idan manomi ya yi asara ya kuma dukkan  bi dukkan ka’idojin da suka kamata wajen noman nasa, to wannan Hukuma tare da kamfanin inshora za su biya shi kashi saba’in daga cikin dari na yawan asarar da ya yi. Shi kuma manomi ya dauki asarar kashi talatin daga cikin kashi dari.

Sai dai inda gizo ke yin sakar shi ne, ga tsari mai kyau, amma dai hanyar da takamata a bi domin tsarin ya kai ga manomin ita ke da matsala. Saboda sai ya zamanto tamkar an gudu ne amma ba a tsira ba. Maimakon a rage cin hancin, sai ya zama yanzu kayan ma ba sa zuwa hannun manoman gabadaya.

Saboda haka zarin da ake kansa yanzu shi ne, dole sai an bi ta hanyar NIRSAL, sannan su kuma su tura sunayen manoma zuwa Babban Bankin Nijeriya, bayan sun karbi wadannan sunaye, sai su turowa da NIRSAL  sakamakon. Ita kuma NIRSAL ita za ta tura wadannan kudade zuwa bankunan kasuwancin da manoma suka bude asusun ajiya a cikinsa. To kafin a yi haka ana shan wahala matuka. Saboda wannan matsalace ma a bara manoman da suka nemi wannan rance daga cikin kashi dari, wadanda suka samu ba su wuce kashi goma ba, saura kashi casa’in duk ba su samu ba. Domin kuwa an bayyyana wata ka’ida mai tsaurin gaske ta cewa dole ne manoma sai sun hada hekta dari biyu da hamsin a wuri daya, sannan suka cancanta a dauki kudi a ba su. kuma ma fi yawan manomanmu gonakin gado suke nomawa kanana, to ta ya ya za a ce sai an hada hekta dari biyu da hamsin, ina manomanmu za su iya hada wannan, bisa wannan dalili ne ya sa manomanmu da yawa suka rasa wannan tallafin na gwamnati.

Saboda haka a wurare, irin namu na Kano, in ba hamshakin manomi ba, ba wanda zai iya cika wannan ka’idar. Saboda haka yanzu kokarin da muke yi shi ne muna kira ga NIRSAL da su sassuto da wannan ka’ida ta su domin manufar da gwamnatin tarayya ke da ita na bunkasa noma don wadata kasa da abinci da samar da ayyukan yi ya samu nasara.

A sunayen da muka bayar na farko, sai da muka kai matakin karshe na sa hannu a fitar da kudi, sai aka ce wai an samu matsala, sabo da haka daga wannan lokaci shi ke nan, magana ta lalace, sai muka tsammaci daman suna nema hanyar hana wadannan kudade ne, wanda kuma tabbas yin hakan tamkar yi wa shirin gwamnatin tarayya na bunkasa noma da wadata kasa da abinci da samar da ayyukan yi zagon gasa ne.

Haka kuma akwai yarjeniyar da manomanmu suka yi na yi noma wanda kamfanin Dangote zai saye, domin a baya manoma na kokawa da rashin samun kasuwar kayan da suka noma, saboda haka bisa wannan tsarin sia ya zama, a kan samu masu sayen amfanin da manoma za su noma. A wannan karon sai rijiya ta bayar da ruwa goga ya hana. Domin kuwa manoman sun kasa samun rancen da za su yi wannan noma.

Abin da ya ba ni mamaki shi ne, sai ita wannan Hukuma ta NIRSAL wadda ba ta ba mu kudin da muka bukata a wajenta ba, domin bunkasa wannan sana’a ta mu ba, sai  ga shit a kira ni Abuja ta ba ni shaidar yabo na cewa, wai an yaba da kwazona kan yadda na gudanar da aikina. Na rasa wane aiki na yi? domin bas u ba mu kudi ba ma ballanta su ga yadda muka sarrafa su, wanda daga nan ne in sun ga shugabancin da na yi ya haifar da kyakkyawan sakamako sai su yaba min. Amma ni da kaina sai da na ji kunyar karbar wannan takardar shaida, domin na san, ban yi aikin da za a ba ni wannan takardar shaida ba. Sannan kuma ga wasu na iya tunanin cewa, kamar ni ma da hadin bakina wajen yi wannan shiri na  bai wa manoma rance zagon kasa. Wasu na iya ganin cewa, kamar  ni ma an hada baki da ni. Wannan shi ne abin da ke damuna, kuma yake damun wasu daga cikin wadanda suka san halin da ake ciki.

A karshe, mece ce mafita dangane da wadannan matsaloli?

Mafita a nan ita ce, tun da gwamnatin na da kyakkyawar manufar taimakawa manoma, to ya kamata hukumomin da aka bai wa alhakin tafiyar da wannan shiri su tabbatar da cewa, tallafin da ake bukatar yi, ya kai ga manoma. Domin kuwa ta haka ne kawai al’amura za su yi kyau, manoma za su amfana.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: