Connect with us

MAKALAR YAU

Kwankwaso: Dan Siyasar Da Babu Kamarsa A Arewa?

Published

on

Masu iya magana su ka ce, yabon gwani ya zama dole, koda kuwa kuna da sabani da shi ta wani bangare ne na rayuwa.

Kusan zan iya cewa kai yara ko kuma dalibai kasashen waje domin yin karatu yana daya daga cikin wasu ayyuka da gwamnatoci sukeyi tun daga gwamnatin tarayya da kuma gwamnatocin jihohi wanda hakan wani tsari ne na kawo cigaba acikin al’umma.

Jihar Kano tana daya daga cikin jihohin da suke kurbar romon dimokradiyya musamman idan akayi Magana ta daukar ‘yan asalin jihar domin zuwa kasashen waje karayu daga digiri na farko dana biyu har dana uku.

Tsohon gwamnan jihar Kano Alhaji Abubakar Rimi, shine wanda yafara kirkiro wannan tsari a lokacinsa kuma bayan ya tafi gwamnatoci da dama sunzo sun dora akan inda ya tsaya irinsu Sabo Bakin Zuwo da Sauransu.

Sai dai zamu iya cewa kowacce gwamnati tana da tsarin yada take daukar nauyin wannan aiki na kai dalibai karatu kasashen waje amma kuma babban dalili wanda kowa akansa yake dorawa shine ana kai wadannan dalibai ne domin ganin jihar ta cigaba kuma ta goga kafada da kafada da ragowar jihohi irinsu jihar Legas wajen cigaba.

Gwamna Sabo Bakin Zuwa shima yayi kokari wajen kai dalibai ‘yan asalin jihar Kano Karatu inda kuma an samu biyan bukata domin an samu mutane da dama wadanda suka samu damar zuwa karatun kuma suka dawo suka cigaba da amfanar da mutanen jihar Kano.

A lokacin gwamnatin Kwankwaso, bayan ya dawo mulkin kano a karo na biyu daga shekara ta 2011 zuwa 2015, Kwankwaso ya tura dubunnan dalibai daga jihar Kano inda sukaje sukayi karatu a fannoni da dama na ilimi a kasashe daban-daban na duniya kuma wasu daga cikinsu sun dawo Najeriya yayinda wasu kuma suka cigaba da zama a kasashen da sukayi karatun sakamakon damarmakin da suka samo na zama a kasashen.

“Mun turaku kuje kuyi karatu domin ku dogara da kanku sannan kuma ku taimakawa mutanen jihar Kano da Najeriya gaba daya da abinda kukaje kuka karanta sannan kuma ina baku shawara idan kun samu damar yin aiki a inda kakayi karatu kuyi amfani da wannan damar” wannan itace maganar da Kwankwaso ya gayawa dalibai kashi na farko da gwamnatinsa ta tura a baya a lokacin da yake ban kwana dasu a gidan gwamnatin Kano.

Wasu daga cikin daliban sun kammala karatuttukansu sun dawo Najeriya suna cigaba da harkokinsu yayinda wasu suka zama malaman makaranta wasu kuma suka dogara da kansu wasu kuma suka kama aiki da hukumomin da ba na gwamnati ba.

Sai dai kamar kowacce gwamnati an samu matsaloli bayan tafiyar gwamnatin ta Kwankwaso musamman wajen cigaba da biyawa daliban da aka tura kudin makaranta  bayan da gwamnatin data gaji gwamnatinsa ta bayyana cewa anyi coge sannan kuma akwai kura kurai akan maganar tura wadannan yara.

Har yanzu akwai daliban da suke kasashen waje kuma ba’a kammala biya musu kudin makarantar ba sakamakon sabani da aka samu tsakanin Kwankwaso da gwamnatin da take ci sannan kuma abubuwa da dama na siyasa sun shiga cikin lamarin daliban da har yanzu suke faman rokon gwamantin Kano akan biya musu kudaden nasu domin su dawo gida.

A satin daya gabata ne dai tsohon gwamnan na Kano, Injiya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ya kammala shirye shiryensa na kai wasu daga cikin dalibai kusan 270 ‘yan asalin jihar nan, wadanda suka fita da mataki mai daraja ta farko wato (First Class) a makarantun da suka gama domin turasu kasashen waje cigaba da digiri na biyu wanda hakan ya biyo bayan kammala tantance daliban tun farko.

Kwankwaso ya kafa gidauniyar tallafawa wadannan dalibai domin tara kudin da za’a biya musu kudin makaranta kuma sakamakon taron kafa wannan gidauniya an tara miliyoyin kudin da za’ayi amfani dasu ta hannun manya manyan ‘yan siyasar Kwankwasiyya da kuma manya mayan ‘yan kasuwa na jihar nan dama jihohin da suke cikin kasar nan.

Yayinda abubuwa suka tabarbare a kasar nan musamman rashin aikinyi da yayiwa kasar nan katutu wannan yunkuri da Kwankwaso yayi zai taimakawa wadannan yara wajen dogaro da kansu ta hanyar yin amfani da abinda suka karanta ba tare da dogaro da gwamnati ba.

Har ila yau wasu daga cikin daliban za su iya samun aiki  a inda sukaje karatun kamar yadda kashi na farko sukayi a shekarun baya kuma zasu kasance sun zama ma’aikata a wadannan kasashe hakan yana nufin an samu aikinyi a tsakanin wadannan yara sannan kuma an samu raguwar cinkoson marasa aikinyi a jihar.

Idan kuma muka kalli abin ta fuskar ilimi zuwan wadannan dalibai kasashen waje zai taimakawa makarantun kasar nan ta hanyar samun kwararrun malaman da zasu dawo domin taimakawa makarantun da suke kasar nan ba kawai jihar Kano ba.

Har ila yau samun masu ilimi a cikin kasa zai taimaka wajen rage aikata muna nan laifuffuka saboda yawancin masu aikata laifi akwai karancin ilimi da kuma rashin aikinyi a tattare dasu sannan kuma zai taimakawa al’ummar jihar Kano wajen samun al’umma mai cikakken tunani mai kyau da kuma fito da hanyoyin cigaban jama’a.

Haka kuma idan muka kalli abin ta bangaren siyasa zamuga wannan yunkuri da Kwankwaso yayi wani sabon lissafi ne na siyasa wanda ya shigo dashi ta hanyar tallafawa matasa da ilimi wadanda kuma matasan nan sune kashin bayan kowacce al’umma kuma duk inda akace matasa suna son abu ko kuma wani dan siyasa tabbas wannan abin ko dan siyasar zaiyi karko.

Yana daya daga cikin abubuwan da Kwankwaso da ‘yan Kwankwasiyya suke alfahari dashi kuma dan takarar gwamnan jihar Kano, Abba K Yusuf yayi yakin neman zabe dashi wato kai yara karatu kasashen waje kuma matasa da dama suna bin tafiyar kwankwaso ne saboda wannan dalili.

Kafin babban zaben shekara ta 2019 da aka gudanar a watannin baya kungiyar Kwankwasiyya tanada kungiyoyi da dama a karkashinta wanda kuma daya daga cikin wadannan kungiyoyi akwai kungiyar dalibai wadanda Kwankwaso ya tura kasashen waje karatu kuma sun bada gudaunmawa sosai a yakin neman zaben Abba Kabir Yusuf wanda yayi takara a karkashin jam’iyyar PDP.

Babu wani abu da zaka bawa matasa a wannan lokaci wanda ya wuce ilimi kuma duk wanda ka bawa ilimi bazai taba mantawa da kaiba a rayuwarsa saboda ta hanyar ilimi duk wani wanda yazama wani abu a duniya zaka iya zama kamarsa.

A halin da ake ciki Kwankwaso yana daya daga cikin manyan ‘yan siyasa a kasar nan sanann kuma  a arewacin kasar nan idan ana maganar dan siyasa wanda zai iya tara mutane masu zabe tabbas kwankwaso bashi dana biyu.

Idan muka duba zamuga wadanda suka samu damar zuwa karatu a lokacin da kwankwaso yana gwamanan jihar Kano yanzu dayawa daga cikinsu sun zama wasu mutane domin wasu sun zama malaman makarantun gaba da sakandire wasu kuma sun zama manyan ma’aikata a kamfanunuwa daban daban ciki har da wadanda suka zama matukan jirgin sama da likitoci da wadanda yanzu suna zaune kasashen waje suna aiki ko kuma suna kasuwanci.

Banda jihar Kano, Kwankwaso dan siyasa ne wanda yake da dubunnan magoya baya a ragowar jihohin da suke arewacin kasar nan musamman yadda yake tallafawa harkokin ilimi da kuma yadda ya kawata jihar Kano da gine-gine na gadojin sama dana kasa da kuma bude makarantun gaba da sakandire dana koyon sana’a sannan kuma uwa uba shine gwamna na farko kuma na karshe a jihar Kano daya kirkiro jami’u guda biyu da suka hada da jami’ar Kimiyya da Fasaha dake garin Wudil da kuma Jami’ar Northwest Unibersity dake cikin birnin Kano.

Kwankwaso ya zama jagora kuma jigo a siyasa musamman a arewacin Najeriya kuma yana kafa wani tushe wanda nan gaba tureshi zaiyi wahala ta hanyar taimakawa matasa suyi ilimi wanda kuma nan gaba matasan sune zasu kasance shugabannin wannan kasa.

Wannan sharhi ya fito ne daga Sunusi Oscar 442 wanda ake yi wa lakabi da Kwankwaso Kannywood.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: