Connect with us

MAKALAR YAU

Shin Buhari Ko Da Gaske Ya Ke Kan Cin Hanci?

Published

on

Sama da shekaru hamsin, Shugaba Buhari ya gina sunansa a matasayin wanda ke kyamatar cin hanci da rashawa, dalilin da ya sa talakawa ke goyon bayansa a ko’ina. Babu wani shugaba a tarihin Nigeria da ya taba samun tsagwaron soyayya irin wadda Buhari ya samu. Zan iya cewa cikin jerin shugabanni a kasashen duniya da ke raye a yau, babu wanda zai iya hada kafada da Buhari wajen irin soyayya da talakawansa ke nuna masa. Hakan ya fito kururu idan mu ka yi la’akari da irin tarbar da ya rika samu a jihohin Nigeria lokacin yakin neman zabe na 2015 da na 2019.

Kafin mu iya amsa tambayar da wannan mukala ta jeho, dole sai mun yi waiwaye cikin shekaru hudun da su ka gabata na mulkin Buhari. A bayyane ya ke cewa daga zuwansa ya yi kokarin hade duk asusuwan gwamnatin tarayya zuwa asusu guda (TSA) abinda ya rage zurarewar kudade daga lalitar gwamnati. Sannan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta dauko tsoffi tare da bude sabbin shari’o’i na manya a kasar duk da cewa kawo yanzu ko guda ba ta iya cimma ga samun nasarar yanke hukunci ba. Kowa ya san yadda sashen shari’a ke kawo tarnaki da tafiyar hawainiya ga shari’o’i. Sannan bangaren majalisa su ma sun dakile wasu mahimman dokoki da za su taimaka gaya wajen yaki da cin hanci.

Ranar lahadi na sami gayyata ta gaggawa daga abokina Auwal Rafasanjani domin halartar taron manema labarai da ya kira a ofishinsu na CISLAC da ke Abuja. Ina isa wajen taron na tarar da yan jarida cike a wurin kama daga gidajen talabijin, Rediyo da jarida. Rafsanjani ya bude taron da cewa “Nigeria na cikin rigima…domin nan da sati guda idan Shugaba Buhari bai saka hannu a kan kudirin dokar kamfanoni ba, zamu kunyata a idon duniya” ya ci gaba da cewa “Wannan doka tun 2018 yan majalisa su ka sahale mata kuma su ka tura wajen shugaban kasa amma kawo yanzu bai sa mata hannu ba. An zabi shugaba Buhari saboda imanin cewa zai yaki cin hanci da rashawa amma sai gashi doka mai mahimmanci a wannan yakin ya zama shine wanda ke dakile ta saboda kin saka mata hannu”

Ita wannan doka ta yi tanadin cewa a samar da bayanai na duk wadanda ke da hannu cikin duk wani kamfani da aka yi wa rajista a karkashin dokokin kasar nan, yadda al’umma za su iya sanin wa ke da hannu cikin kowanne kamfani. Idan Shugaba Buhari ya sa ma ta hannu, hakan zai bada damar samar da kundin da za’a lissafa wadannan bayanai na kamfuna a watsa shi a yanar gizo yadda kowa zai iya bincika ya sani. Kamar yadda Rafsanjani ya nuna, rashin saka wa wannan doka hannu zai lalata yunkurin sama da shekaru goma da kungiyoyi su ka yi ta fafutuka wajen ganin an samar da ita. Ya kara da cewa har ma’aikatar harkokin wajen Amurka da majalisar turai sun ziyarta domin ganin an samar da wannan doka. Idan Buhari bai saka mata hannu ba hakika hakan zai rage kimarsa a idon kasashen duniya kuma kasar za ta yi asarori da dama, ciki har da kora daga cikin kungiyoyin duniya da su ka saka hannu kan dokar yin harkokin masana’antu a bude (Global Edtractibe Industry Transparency Initiatibe) a karshen wannan shekara ta 2019.

Gwamnatin nan ta nuna hazaka wajen tallafawa kananan sana’o’i ta hanyar samar da bashin manoma, da na NIRSAL da kuma na harkokin fasaha, idan a ka saka wa dokar hannu zata bunkasa kananan sana’o’i domin zai ba da damar mutum guda zai iya yin rajistar kamfani sabanin a baya sai yana da masu hannu jari da daraktoci.

Wani kudurin kuma da ya danganci yaki da cin hanci da rashawa shine na hana almundahanar cin hanci (Prebention of Corruption Amendment bill) wanda shi ma yan majalisu sun sahale masa kuma ya na teburin shigaban kasa amma bai saka masa hannu ba. Haka nan kudurin binciken bayanai na ma’aikatu da ma’aikatan gwamnati (Federal Audit Sebice Bill) wanda zai bawa baban mai bincike na kasa (Auditor General) damar hukuntu duk wata ama’aikata ko ma’aikaci da ya ki mika bayanansa domin a bincika. Inda wannan kuduri ya fi sauran tasiri shine maimakon jiran sai kotu ta yanke hukunci, Babban mai bincike na kasa zai sami damar hukunta masu irin wannan laifi kai tsaye ta hanyar rike kudadensu. Saka wa wannan kuduri hannu zai sa ma’aikata da maikatu su shiga taitayinsu nan take sabooda sun san hukunci za’a yi musu kai tsaye.

Don Allah idan Buhari da gaske ya ke a yakinsa da cin hanci da rashawa ina dalilin da zai kasa saka wa wadannan kudure-kudure hannu? Kuma a dokar kasa cikin kundin tsarin mulki na 1999, shugaban kasa na da kwanaki talatin bayan an mika masa kuduri daga majalisa da ko dai ya yarda da shi ko ya ki yarda ya mayarwa da majalisia. Sai gashi duk wadannan kudure-kudure sun share sama da watanni shida a gaban shugaban kasa ba tare da ya ce komai ba.

Tarihi ya nuna mana yadda cikin yan makonni da hawan shugaba Yar Adua mulki, ya saka wa kudurin bada kwangila hannu, abinda ya kawo gagarumin canji wajen rage yadda ake badakala wajen bayarwa da aiwatar da kwangilolin gwamnati. Wannan abu da Yar Adua ya yi, ya sa ya kafa tarihi a sashen kafa dokoki da ke yakar cin hanci da rashawa. Shin da ace shugaba Buhari ya fadi a zaben 2019, wane abu guda zai nuna wanda ya zama abin tarihi da ya kafa a sashen dokoki da ke yakar cin hanci da rashawa? A cikin shekaru hudu da su ka gabata mun yi ta zargin majalisun tarayya da dakile manufofin wannan gwamnati amma sai ga shi a zahiri cewa gwamnatin ce da kanta ke dakile kokarin magance cin hanci da rashawa ta bangaren yin dokoki. Wannan na nuna cewa akwai hannun wasu shafaffu da mai cikin gwamnati da ba sa son wadannan kudure-kudure su kai gaci. Don haka babu dalilin da zamu yi wa shugaba Buhari uzuri, saboda gazawarsa a wannan bangare. A kalla ya kamata a ce bayan kwanaki 30 da kundin tsarin mulki ya tanada, idan shugaba Buhari da mutanen gwamnatinsa na da wata suka game da kudurin da sai ya mayarwa majalisa da korafe-korafensa amma ba ya rike shi ba.

A karshe muna kira ga shugaba Buhari ya gaggauta saka wa wandannan kudure-kudure hannu ciki gaggawa, musamman na kamfuna wanda sati guda ya rage wa kasar nan kafin wa’adinsa ya cika, idan kuma bai yi haka ba, to hakika ya tabbatarwa da yan Nigeria cewa yakinsa a bangaren cin hanci yaudara ne kawai ba gaskiya ba. Kuma kada shugaba ya manta cewa yan Nigeria da sauran kasashen duniya da kuma mahaliccinsa sun sa ido su ga ko zai saka wa wadannan kudure-kure hannu ko kuwa a’a.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!