Connect with us

LABARAI

Kafin 2023 Za Mu Farfado Da Matatun Fetur Din Nijeriya- Kyari

Published

on

Sabon shugaban kamfanin albarkatun man Nijeriya wato NNPC, Mele Kyari, ya sha alwashin gyara dukkanin matatun man kasar, kafin karewar wa’adin gwamnati mai ci a shekarar 2023. Mele Kyari ya dauki alkawarin ne bayan karbar jagorancin kamfanin na NNPC daga Dakta Maikanti Baru.

Kyari ya kara da alwashin farfado kara yawan litar man da matatun kasar za su rika tacewa zuwa lita miliyan 3 a kowace rana.

Gwamnatin Nijeriya da suka gabata, sun narka makudan kudade kan kokarin farfado da matatun man kasar da suka durkushe amma hakan bata samu ba. Haka zalika gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari mai ci a zangon farko ta yi kokarin gyara matatun man, amma suka gaza kaiwa matakin da ake bukata.

A halin yanzu matatun man Nijeriyar da ke Warri, Fatakwal, da kuma Kaduna, na iya tace litar danyen mai dubu 445 ne kawai, a wasu lokutan ma adadin ya kan gaza, saboda matsalolin lalacewar wasu kayayyaki.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: