Connect with us

LABARAI

A Fifita Auren Mata Masu Tarbiyya Fiye Da Komai – Shattemah

Published

on

An shawarci samari ko matasa masu shirin yin auren fari ko kuma magidanta masu son yin kari da ya fi mayar da hankali wajen neman mace mai tarbiyya da kuma kula da addini fiye da sauran abubuwan da su ka halasta a auri mace, kamar kyau, kudi da dai sauransu.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin wani dan kasuwa, Alhaji Ashiru Ali Mohammad Yammusa Shattemah, a lokacin wata gagarumar walimar aure wacce addinin Musulunci ya yarda a yi ga masu iko ko halin yi a duk lokacin da a ka gabatar da auren wani ko wata.

Yammusa ya kara da cewa, addinin Musulunci ya bayyana cewa, a na iya auren mace don dalilai daidai har guda hudu, wasu na auren Mace don kyawunta ko don nasabarta ko don dukiyarta ko kuma don Addininta.

Amma akwai Hadisin da kuru-kuru ya bayyana cewa, auren ma’abociyar Addinin shi ne ya fi, ma’ana mai tarbiya da tsoron Allah wadda kuma take kaunarka, a nan ne za ka ci moriyar auren domin kyau da sauran wadansu abubuwa na gushewa, amma tarbiyya irin ta Addinin Musulunci ba ta taba gushewa har abada.

Don haka, duk wanda ya tashi yin aure, ya tabbata ya fifita kyakkyawar tarbiyya da kuma lura da inda wacce yake son aurar ta fito. Daga nan ne kuma, ya yaba wa dubban mutanen da suka samu halartar wannan gagarumin taro, da ya hada da Sarakuna, Malaman Addini, ‘Yankasuwa, Masu rike da Mukaman siyasa da dai sauran su, a cewar tasa.

Haka zalika, a nasa jawabin Dattijo Alhaji Mohammad, ya aiwatar da tasa nasihar a kan muhimmancin kula da iyali, musamman ta fuskar lura da amanar da aka damka maka tare da tausaya musu kamar yadda Allah (SWT), Ya yi umarni shi. Haka nan, a bangaren sadar da zumunci wanda mai yinsa ba ya taba yin mummunan karshe. Sannan ya sake jan hankalin al’umma bisa koyi da magabatanmu wadanda suka rike zumunci, suka kuma yi kyakkyawan karshe.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: